Access, GTB, UBA, Da Sauran Bankuna Sun Wawure N156bn Daga Asusun Jama’a, Sun Tura Wa Gwamnati

Access, GTB, UBA, Da Sauran Bankuna Sun Wawure N156bn Daga Asusun Jama’a, Sun Tura Wa Gwamnati

  • Wani sabon bincike ya nuna yadda bankuna suka biya gwamnatin tarayya sama da naira biliyan 100 matsayin haraji (VAT)
  • Bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade sun biya kudin harajin ne daga watan Janairu zuwa Satumba
  • Ana sa ran bankuna za su cire kudin daga asusun kwastomomi kamar yadda tsarin haraji ya ke tare da kaso 5% na harajin VAT

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade a Najeriya sun saka naira biliyan 156.94 matsayin kudin harajin VAT a asusun gwamnatin tarayya.

Wannan adadin kudin ya karu da kaso 13.63% idan aka kwatanta shi da naira biliyan 78.77 da bankunan suka tura wa gwamnati a shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan gwamnatin tarayya sun yi bikin Kirsimeti ba tare da albashin Disamba ba

Bankuna sun biya gwamnati harajin N156.9bn a 2023.
Access, GTB, UBA, da sauran bankuna sun tura wa gwamnati harajin sama da naira biliyan 100 a 2023. Hoto: Access
Asali: Facebook

Hukumar kididdiga ta kasa ta hannun hukumar tattara haraji ta kasa (FIRS) ta fitar da sabon kiyascin kudin harajin da cibiyoyin hada-hadar kudaden suka biya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ake nufi da harajin VAT na bankuna?

Harajin VAT na a dokar haraji ta V1 LFN 2004 (kamar yadda aka sabunta) wanda aka fi sani da harajin ayyuka da cinikayya da aka gudanar, inda ake cire kaso 7.5%.

Ana so dukkan bankuna da cibiyoyin kudi amma ban da bankunan 'community', cibiyoyin ba da lamunin gidaje da sauran su, za su biya gwamnati harajin kudaden da suke cajar kwastominsu.

Yadda bankuna suka biya gwamnati haraji a 2023

Wani bincike da Legit ta yi ya nuna cewa a watan Janairu zuwa Maris 2023, an wawure naira biliyan 35.40 daga asusun jama'a an saka a asusun gwamnati matsayin haraji.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta fara tuhumar wasu manyan ministocin Buhari kan badakalar naira biliyan 187

A watanni hudu na tsakiyar shekarar 2023, bankuna da cibiyoyin kudi sun biya gwamnati harajin naira biliyan 57.26, yayin da suka biya naira biliyan 64.27 a watanni hudu na karshen 2023.

Gwamnati za ta saki sunayen 'yan Najeriya da za ta ba tallafin N50,000

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta sanar da lokacin da za ta saki sunayen wadanda za su ci moriyar shirin shugaban kasa na tallafin naira dubu hamsin

Minsitar jin kai da kawar da fatara, Betta Edu ta sanar da cewa a watan Janairu 2023 kowa zai san wanda ya shiga cikin shirin da aka fara a watan Disamba

Gwamnatin Tinubu ta kawo wannan shiri don rage wa 'yan Najeriya radadin cire tallafin man fetur, musamman talakawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel