Tsohon Mataimakin Gwamnan CBN Zai Yi Bayani Kan Yadda Emefiele Ya Mallaki Bankin Union

Tsohon Mataimakin Gwamnan CBN Zai Yi Bayani Kan Yadda Emefiele Ya Mallaki Bankin Union

  • Bincike kan yadda Godwin Emefiele ya mallaki bankin Union ya dauki sabon salo yayin da aka gayyaci shugaban bankin Titan Trust
  • Babban mai bincike kan badakalar da aka tafka a CBN na zargin an yi amfani da Babatunde Lemo da wasu wajen mallakar bankin
  • Ana tuhumar tsohon gwamnan CBN da tafka almundahanar biliyoyin kudade tare da mallakar bankin Union da Keystone ba bisa ka'ida ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Babban mai binciken badakalar da aka tafka a babban bankin Najeriya, Jim Obazee ya gayyaci shugaban bankin Titan Trust (TTB), Babatunde Lemo kan zargin sa hannu wajen mallakar bankin Union.

An umurci Lemo, wanda tsohon gwamnan bankin CBN ya gurfana gaban hukumar jami'an fikira a Abuja a ranar Alhamis, 28 ga watan Disamba, rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki yayin da matar tsohon shugaban PDP da surukarsa suka mutu a jajiberin Kirsimeti

Tunde Lemo zai gurfana gaban kwamitin binciken badakalar CBN
Tsohon mataimakin gwamnan CBN zai yi bayani kan yadda Emefiele ya mallaki bankin Union. Hoto: @Imranmuhdz, @GodwinIEmefiele
Asali: Twitter

An kuma nemi shugaban TTB ya taho tare da masu tallata bankin, Messrs Cornelius Vink da Mr Rahul Savara, don ganawa da tawagar masu binciken.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati na binciken Godwin Emefiele kan badakala a CBN

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa a ranar 24 ga watan Disamba ne aka aike wa Lemo takardar gayyatar mai dauke da sa hannun shugaban hukumar sashen bincike na musamman.

Babban mai bincike ya ba da rahoton cewa akwai wadanda tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele yayi amfani da su wajen kafa bankin Titan Trust don mallakar bankin Union.

A watan Yuli 2023 ne aka nada Obazee matsayin mai bincike na musamman, kuma ya gabatar da rahoton binciken sa mai taken "Rahoton bincike na musamman kan CBN da sauran su (manyan laifuka)"

Obazee ya mika rahotonsa ga shugaban kasa Bola Tinubu a Larabar da ta gabata, inda ya gano yadda aka mallaki bankin Union da Keystone, bisa kitsawar Emefiele tare da wasu.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan CBN ya ƙara bankado muhimmin abu kan Emefiele a mulkin Buhari da Jonathan

An gano yadda Emiefele ya hada kai da wasu wajen saye bankuna uku

A wani rahoton binciken da aka gudanar kan CBN, an gano yadda Godwin Emefiele ya kwashi kudi ya mallaki bankuna har guda uku.

Jim Obazee, mai bincike na musamman da aka naɗa kan lamarin ya mika rahoto ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ranar Laraba, Legit Hausa ta ruwaito.

A cikin wannan rahoton, ya zargi Emefiele da amfani da wakilai wajen sayen bankin Union, Polaris da Keystone.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel