Jos
Da safiyar yau Laraba ne aka bindige wani jami'in ɗan sanda a cikin kasuwa a karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Plateau yayin hana cinikayya a bakin titi.
Gwamnatin jihar Filato ta ba masu sayar da shanu wa'adin mako biyu domin su tashi daga kasuwar Kara da ke Bukuru. Yan kasuwar sun koka kan matakin.
Wasu ƴan banga sun cafke wani matashi da bam daure a cikinsa yana kokarin tayarwa a garin Dadin Kowa da ke Jos ta Kudu a jihar Plateau a jiya Litinin.
Kungiyar kwadago ta yi barazanar rufe ofisoshin kamfanonin raba lantarki a fadin kasar nan, har sai gwamnatin tarayya ta janye karin kudin wutar.
A yayin da wa'adin da kungiyoyin kwadago ta ba hukumar NERC ya kare, mambobin NLC da TUC sun fara rufe ofisoshin kamfanin rarraba wutar lantarki da ke fadin Nigeria.
Tsohon Ministan wasanni a mulkin Muhammadu Buhari, Solomon Dalung ya koka kan yadda aka yi watsi da shi a asibitin Jos kan N80,000 kacal wanda likita zai duba shi.
Farashin garin kwaki ya tashi a kasuwar Katako dake birnin Jos na jihar Plateau. A halin yanzu ana sayar da buhu N72,000 yayin da mudu ya kai N1,100.
Wata 'yar jarida, ta bankado yadda wani likitan boge ke zubar wa 'yan mata ciki a unguwar Yan-Doya da ke Jos, jihar Plateau a kan N5,000 tare da jefasu a karuwanci.
Sakamakon ta'adin da wasu bata gari da suka yi na lalata hasumiyoyin da suke dauke da layukan wutar lantarki a hanyar Jos, jihohi uku sun shiga duhu a Arewa.
Jos
Samu kari