Gwamna Ya Dauki Tsattsauran Mataki Kan Masallatai da Coci a Plateau, Ya Kakaba Doka

Gwamna Ya Dauki Tsattsauran Mataki Kan Masallatai da Coci a Plateau, Ya Kakaba Doka

  • Gwamna Caleb Mutfwang ya haramta tare hanyoyi da ake yi yayin ibadar Musulmai ko Kiristoci a fadin jihar baki daya
  • Bayan wannan sabon umarni, gwamnan ya kuma bukaci binciken takardun amincewa da gina wuraren ibada daga hukumar JMDB
  • Wannan mataki bai rasa nasaba da yawan korafi da jama'a ke yi lokacin ibada a masallatai ko coci da ake rufe hanyoyi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Gwamnatin jihar Plateau ta dauki mataki kan masallatai da coci da ke tare hanyoyi yayin ibada.

Gwamna Caleb Mutfwang shi ya tabbatar da haka inda ya ce ya haramta kange hanyoyi da ake yawan samu a jihar lokacin ibada.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Kungiyar Lauyoyin Arewa ta fadi sahihin Sarkin Kano bayan yanke hukunci

Gwamna ya dauki mataki kan masallatai da coci kan tare hanyoyi
Gwamna Caleb Mutfwang ya haramta tare hanyoyi da masallatai da coci ke yi a Plateau. Hoto: Caleb Mutfwang.
Asali: Facebook

Gwamna ya hana Musulmai, Kirista tare hanyoyi

Daily Trust ta ruwaito cewa Caleb ya kuma bukaci duka wuraren ibada su mika takardun amincewa da hukumar kula da birane (JMDB) ta ba su yayin gina wuraren ibadun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta bakin babban manajan hukumar, Hart Bankat.

An rubuta takardun ga kungiyar Kiristoci ta CAN da Jama'atul Nasril Islam (JNI) da ke jagorantar addinan biyu, cewar BusinessDay.

Sakataren kungiyar Jama'atu Nasril Islam, JNI a jihar, Dakta Salim Musa Umar ya tabbatar da samun takardar.

Sanarwar haramta tare hanyoyin ta bukaci shugabannin addinai su gargadi mambobinsu domin bin umarnin yadda ya kamata.

Sanarwar haramta tare hanyoyi a Plateau

"Bayan rattaba hannu a dokar a ranar 1 ga watan Maris 2024, ina mai sanar da ku haramta tare hanyoyi da wuraren ibada ke yi."

Kara karanta wannan

CAN ta roki Musulmai bayan Fasto ya farmaki Musulmi kan yanka ragon layya

"Muna ba da shawarar duka wuraren ibada su samar da isasshen wuri domin ajiye ababan hawa yayin ibada nesa da manyan hanyoyi."
"Duka wuraren ibada za su kawo takardun amince musu yin gini da hukumar JMDB ta ba su domin gudun fuskantaar hukunci."

- Cewar sanarwar

CAN ta hukunta Fasto kan dukan Musulmi

Kun ji cewa Kungiyar Kiristoci a Najeriya (CAN) reshen jihar Oyo ta roki gafarar al'ummar Musulmai a jihar kan abin da wani Fasto ya yi.

Kungiyar ta yi rokon ne bayan wani Fasto ya farmaki wani magidanci da matansa biyu kan yanka ragon layya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.