Ahmad Musa Zai Yi Amfani da Kwallo a Kawo Zaman Lafiya a Filato, Ya Gana da Gwamna

Ahmad Musa Zai Yi Amfani da Kwallo a Kawo Zaman Lafiya a Filato, Ya Gana da Gwamna

  • Shahararren dan wasan kungiyar kwallon kafar Super Eagles ta Najeriya, Ahmed Musa ya dauki mataki domin dawo da zaman lafiya a Filato
  • Ahmad Musa ya bayyana cewa harkar wasannin za ta taka rawa sosai wajen dinke al'umma waje guda da kawo zaman lafiya mai dorewa
  • Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya nemi ganawa da dan kwallon domin ganin sun yi amfani da damar wajen samun zaman lafiya a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau - Shahararren dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa ya fara kokarin samar da zaman lafiya a jihar Filato.

Ahmed Musa ya gana da gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang domin cika burinsa na ganin zaman lafiya ya dawo yankunan jihar.

Kara karanta wannan

Zargin rashin caccakar ƴan adawa: Gwamna ya fatattaki sakataren yaɗa labaransa

Ahmed Musa
Ahmad Musa ya yi kokarin kawo zaman lafiya a Filato. Hoto: Ahmed Musa MON
Asali: Facebook

Legit ta gano haka ne cikin wani sako da Ahmed Musa ya wallafa a shafinsa na Facebook bayan ganawa da gwamnan jihar Filato.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ahmed Musa ya yi kira ga gwamna

Tun a farko, Ahmed Musa ya yi kira ga gwamnan jihar Filato domin ba da gudunmawa kan matsalar tsaro a jihar.

Dan kwallon ya yi kiran ne yayin da ya yi wasa da wasu yara da yake ba horo a harkar kwallon kafa a jihar ta Filato.

Gwamna Caleb ya nemi Ahmed Musa

Biyo bayan kiran da dan wasan ya yi, gwamna Caleb Mutfwang ya neme shi domin su tattauna kan lamarin.

Hakan kuwa ya ba da dama Ahmed Musa ya tattauna da gwamnan a fadar gwamnati kan yadda zai taimaka wajen kawo zaman lafiya a jihar.

Yadda wasanni za su kawo zaman lafiya

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: A karshe, Abba ya fayyace gaskiya kan umarnin cafke Aminu Ado Bayero

Ahmed Musa ya tabbatar da cewa harkar wasannin na taimakawa wajen kawo cigaba da zaman lafiya a cikin al'umma.

Saboda haka ya ce zai yi amfani da harkar kwallo wajen samar da hadin kai tsakanin al'ummar jihar da cigaban matasa domin samar da zaman lafiya mai dorewa.

An karrama Ahmed Musa a Yobe

A wani rahoton, kun ji cewa sarkin Nguru, Alhaji Mustapha Ibn Mai Kyari ya yiwa Ahmed Musa naɗin sarautar gargajiya ta Shetiman Kwallon Kafan Nguru.

Shahararren ɗan wasan ya ziyarci jihar Yobe ne domin ƙaddamar da bude gasar cin kofin The AAJ da aka gudanar a Yobe ta Arewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng