An Shiga Fargaba Bayan Cafke Matashi Dauke da Bam a Jos Yana Kokarin Tayarwa

An Shiga Fargaba Bayan Cafke Matashi Dauke da Bam a Jos Yana Kokarin Tayarwa

  • Dubun wani matashi ya cika bayan cafke shi da bam daure a cikinsa yana kokarin tayarwa a jihar Plateau
  • Lamarin ya faru ne a jiya Litinin 13 ga watan Mayu a garin Dadin Kowa da ke Jos ta Kudu a cikin wani banki
  • Wasu ƴan banga ne suka yi nasarar dakile harin bayan gano shirin matashin wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - An shiga fargaba bayan cafke wani matashi da bam a Jos ta Kudu da ke jihar Plateau.

Wasu mutane ne suka yi nasarar cafke matashin wanda ba a bayyana sunansa ba har zuwa lokacin tattara wannan rahoto.

Kara karanta wannan

Operation kauda badala: Hisbah ta damke maza da mata 20 suna wanka tare a Kano

Matashi ya shiga hannu yana kokarin tayar da bam Jos
An yi nasarar kama wani matashi dauke da bam a Jos da ke jihar Plateau. Hoto: @PoliceNG, @ZagazOlamakama.
Asali: Twitter

An cafke matashi da bam a Jos

Matashin yana kokarin tayar da bam din ne da ke daure a jikinsa a cikin wani wani banki da ke yankin, cewar Zagazola Makama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya faru ne a jiya Litinin 13 ga watan Mayu a garin Dadin Kowa da ke Jos ta Kudu a jihar.

Punch ta tattaro cewa wasu ƴan banga ne suka yi nasarar dakile harin bayan ankara da motsin matashin a kusa da bankin.

Wani ma'aikacin bankin da abin ya faru da ya bukaci a boye sunansa ya ce matashin ya bukaci a ba shi fansar N100m ko kuma ya tayar da bam din da ke daure a jikinsa.

Ya ce matashin ya zo wurin cire kudi inda ya yi barazanar tayar da bam din idan ba a biya masa bukatarsa ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Aliero sun tafka barna, sun hallaka sojoji, jikkata wasu 11 a Katsina

Jos: Matashi mai bam ya sha da kyar

Wasu fusatattun matasa sun farmaki matashin inda suka nemi hallaka shi kafin aka kawo dauki aka kwace shi.

Sai dai har lokacin tattara wannan rahoto ba a bayyana ko matashin da ke kokarin tayar da bam na da alaƙa da wata kungiyar ta'addanci ba.

Daga bisani an dauke shi zuwa ofishin 'yan sanda mafi kusa domin ci gaba da bincike kan lamarin tare da kokarin gano gaskiya kan shirin matashin.

Sojoji sun hallaka kasurgumin ɗan bindiga

Kun ji cewa Rundunar sojojin Nigeria ta hallaka 'yan bindiga hudu a wani farmaki a jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya.

Dakarun 'Operation Whirl Punch da ke Arewa maso Yamma sun yi nasarar hallaka miyagu ciki har da kasurgumin ɗan bindiga, Dogo Bangaje.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel