Masu Sayar da Shanu Sun Koka Kan Korarsu Daga Kasuwa a Jihar Filato

Masu Sayar da Shanu Sun Koka Kan Korarsu Daga Kasuwa a Jihar Filato

  • Kungiyar masu sayar da shanu a jihar Filato ta koka kan matakin da gwamnatin jihar ta dauka na canza musu kasuwa
  • A ranar Litinin da ta wuce ne gwamantin jihar ta ba su wa'adin mako biyu domin su su tashi daga kasuwar Kara da ke Bukuru
  • Legit ta tattauna da wani mazaunin Jos, Al-Amin Aliyu domin jin yadda yanayin zaman lafiya yake a yankin da ake son mayar da kasuwar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Filato - Kungiyar masu sayar da shanu ta kasuwar Kara da ke Bukuru a jihar Filato sun nuna damuwa kan kokarin canza musu wuri da gwammnati ta yi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya za ta sake zama da NLC kan mafi karancin albashi

Shanu jos
Masu sayar da shanu sun koka kan rashin tsaro a sabuwar kasuwar da aka ba su a Jos. Hoto: Arterra
Asali: Getty Images

Hakan ya biyo bayan wa'adin mako biyu da gwamnatin jihar ta ba su ne kan su tashi daga kasuwar.

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa a ranar Litinin da ta wuce ne gwamantin jihar ta ba su wa'adin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka tashi masu shanu daga kasuwa?

Hukumar kula da cigaban birnin Jos ce ta ba su wa'adin tare da bayyana dalilai kan matakin da gwamnatin jihar ta dauka.

Hukumar ta bayyanawa yan kasuwar cewa gwamnatin jihar za ta gina filin wasa ne a wurin da kasuwar ta ke.

Masu sayar da shanu sun yi korafi

Masu sayar da shanu a kasuwar Kura sun koka kan matakin da gwamnatin ta dauka kan mayar da su yankin Gero ko Sabongida.

Sun ce yankunan sun shahara da rikicin kabilanci kuma hakan barazana ce ga masu saye da sayarwa.

Kara karanta wannan

Mata sun shiga tashin hankali bayan 'yan bindiga sun kashe mazajensu a Neja

Matsayar shugaban yan kasuwar shanu

Shugaban matasan kasuwar, Hamza Ahmad Yusuf ya ce ya kamata gwamnatin ta sake duba lamarin.

Shugaban ya ce a yankin da ake so su koma ne aka kashe babban sojan Najeriya, Manjo Janar Idris Alkali.

Saboda haka ya ce idan aka koma yankin ba tabbas dukiyar mutane da rayukansu za su kasance cikin aminci.

A karkashin haka ne yan kasuwar suka bukaci gwamnatin jihar ta sake nazari kan lamarin domin tabbatar da zaman lafiya da cigaba a jihar.

Legit ta tattauna da Al-Amin Aliyu

Legit ta tattauna da wani mazaunin Jos kan yadda zaman lafiya yake a yankin Gero da ake son mayar da kasuwar.

Al-Amin ya shaida cewa ana samun rikicin kabilanci da addini sosai a yankin kuma idan aka mayar da kasuwar wurin to zai zama barazana ga baki masu kawo kaya daga garuruwa.

Sojoji sun yi nasara kan yan ta'adda

Kara karanta wannan

Kwara: Sun fadi gaskiya bayan cafke likita da wasu da zargin satar mahaifa da cibiyar jariri

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta na ci gaba da nuna kwazo da sadaukar da kai a yaki da 'yan ta'adda da masu tayar da kayar baya.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel