Babban Sallah: An Sace Ragon Layyan Babban Limami a Arewacin Najeriya

Babban Sallah: An Sace Ragon Layyan Babban Limami a Arewacin Najeriya

  • Wasu ɓata gari sun sace ragon layya na babban Limamin kauyen Mista Ali a ƙaramar hukumar Bassa a jihar Filato
  • Limamin da ya yi limancin Sallar idi a garin, Malam Haruna Yakub ne ya bayyana haka a cikin huɗuba bayan sallame Sallah raka'a biyu ranar Lahadi
  • Malam Haruna ya nuna damuwarsa da mamakin yadda mutane suka lalace, inda ya tunatar da cewa za a yi kowa hisabi ranar lahira

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Wasu ɓarayi sun sace ragon layya na babban limamin Masallacin garin Mista Ali a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato.

Ɓata garin sun ɗauke ragon ne yayin da ake tsaka da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a daren ranar jajibirin Babbar Sallah a gidan limamin.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun hallaka ƴan bindiga sama da 100 ana shagalin Sallah a Arewa

Satar ragon layya a Jos.
Barayi sun ɗauke ragon layyar babban limami a Jos Hoto: Nur Photo
Asali: Twitter

Malam Haruna Yaqub, wani malamin Addinin Musulunci ne ya bayyana haka a cikin huɗubar da ya yi bayan kammala raka'o'i biyu na Sallar Idi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sacewa Liman ragon sallah

Limamin ya yi Alla-wadai da sace ragon layyar babban Malaminsu, yana kai bayyana lamarin da muguwar ɗabi'a, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

"Jiya daddare aka sace ragon da babban Limaminmu ya sayo domin ya yi layya, lamarin ya tada mana hankali, mun yi mamakin sace ragon Liman.
"Wannan na nufin mutane ba su jin tsoron Allah, yanzu mun yi lalacewar da mutane za su sace ragon da aka saya domin yin ibadar addini,"

- Malam Yakub.

Limamin ya tunawa mutane hisabi

Malam Haruna ya kuma yi kira ga jama’a da su ji tsoron Allah, su daina sata ko aikata wasu miyagun laifuka, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Ka yafewa maƙiya," Matasan Arewa sun aike da saƙo ga Sarki Aminu Ado Bayero

Ya kuma ja hankalin mutane da tunatar da su cewa Allah SWT zai yi kowa hisabin ayyukansa a ranar gobe ƙiyama.

"Wannan shi ne lokacin da ya dace mutane su tubar ma Allah su koma kan tafarki madaidaici, ya kamata mutane sun daina saɓawa Allah, su maida hankali wajen yin ayyukan alheri."

Matasa sun tada hargitsi kan naɗin sarauta

A wani rahoton kuma matasa sun ɗauki zafi, sun farmaki jami'an gwamnati, ƴan sanda da sojoji a wurin bikin naɗin Sarkin Nkomoro a yankin Ezza ta Arewa a Ebonyi

Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya fara ne daga lokacin da wakilin gwamnati ya faɗi sunan wanda za a naɗa a matsayin sabon sarki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262