Farashin Garin Kwaki Ya Yi Tashin Gwauron Zabi a Jos

Farashin Garin Kwaki Ya Yi Tashin Gwauron Zabi a Jos

  • Yayin da al'umma ke kara shiga matsin rayuwa saboda tashin farashin kayan masarufi, kudin garin kwaki ya haura sama a kasuwani
  • Rahotanni da ke fitowa daga Kasuwar Katako dage Jos sun nuna cewa farashin garin kwaki ya yi tashin da ba a taba gani ba cikin shekaru
  • Masu sayar da garin kwaki a kasuwar sun bayyana dalilan tashin farashin tare da yin hasashen yadda zai kasance nan gaba kadan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jos - Garin kwaki na daya daga cikin abincin da 'yan Najeriya ke amfani da shi, musamman masu kananan karfi da dalibai da ke makarantun kwana.

Farashin garinn kwaki ya tashi
Tashin farshin garin kwaki zai kara sa al'umma cikin wahala. Hoto: UGC
Asali: UGC

Yawanci al'umma na amfani da shi ne saboda sauƙin farashinsa da kuma yadda ake sarrafasa cikin sauki.

Kara karanta wannan

Gwamnan CBN ya bayyana abubuwan da ke kawo tashin farashin kayayyaki a yanzu

Farashin garin kwaki a kasuwar Jos

A wani rahoto da jaridar Daily Trust ta fitar, ya nuna cewa farashin garin kwaki ya tashi sosai a birnin Jos na jihar Plateau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna cewa kowanne mudun gari ana sayar da shi a kan N1,100 sannan buhunsa ya kai N72,000.

Masu sayar da garin kwaki sun koka kan cewa cikin shekaru da dama farashin bai taba tashi kamar irin na wannan lokaci ba.

Me ya kawo tashin farashin gari?

Hassan Maigari, wani mai sayar da garin kwaki ya bayyana cewa yawaitar buƙatarsa yana daga cikin abin da ya jawo tashin farashin.

A cewarsa, a halin yanzu al'umma da dama sun dogara ne da garin kwaki a matsayin abinci saboda matsin rayuwa da ake ciki, rahoton News Digest Nigeria.

Amma Abdullahi Ibrahim kuma, ya ce farashin ya tashi ne saboda wadanda suke hada shi su turo kasuwa.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya fayyace abin da ya tilastawa Tinubu cire tallafin man fetur

Ya ce masu aikinsa suna jinkirin hada shi ta inda za a bukace shi ba a samu ba. Hakan sai ya jawo sun kara masa kudi.

Ya farashin zai kasance nan gaba?

Sai dai duk da karin farashin da aka samu, 'yan kasuwar sun bayyana cewa farashin zai iya tashi cikin satuttuka masu zuwa.

Sun bayar da dalilin cewa a nan gaba kadan za a shiga damuna wanda a lokacin ne farashin yake hauhawa bisa al'ada.

Farashi abinci ya fara sauka

A wani rahoton, kun ji cewa farashin wasu kayayyaki kamar shinkafa, sukari, fulawa, taliyar indomi da dai sauran su ya fara sauka a kasuwannin Najeriya.

Masu fashin baki sun nuna cewa hakan ya faru ne sakamakon darajar da Naira ta yi a kan Dalar Amurka da ma sauran kudaden kasashen waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel