Zaben Shugaban kasan Najeriya
Labarin da muke samu ya bayyana cewa, a halin da aka ciki Tinubu ya lashe zabe a rumfar da ya kada kuri'a a jihar Legas. An fadi adadin kuri'ar da ya samu.
Yanzu muke samun labarin yadda wasu 'yan daba suka kai farmaki a wurin aikin zabe, inda suka sace na'urar aikin zabe ta BVAS a jihohin Katsina da kuma Delta.
Yayin da yan Najeriya suka fito don yin zaben shugaban kasa a yau Asabar, 25 ga watan Fabrairu, wasu yan daba sun farmaki rumfar zabe a yankin Ikate dake Lagas.
Wasu yan daban siyasa ne sun kai hari rumfunan zabe a yankin Oshodi da Itire a Legas inda suka tarwatsa masu zabe sannan suka kona akwatin zabe a yau Asabar.
Farfesa Mahmud Yakubu, shugaban hukumar zabe ta kasa INEC ya ve babu wanda za'a hana jefa kuri'a matukar kafin 2:30 na rana yana kan layi a rumfar zabensa.
Jam'iyyar Accord ta janye daga zaben shugaban kasa na ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu inda ta ayyana goyon bayanta ga Peter Obi na jam'iyyar Labour Party.
Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya nuna damuwa da rashin jin dadi bisa yadda na'uarar tantance masu zabe na BVAS ta ki tantance shi da matarsa a wurin zabe.
Wani matashi mai suna Akayama ya gamu da ajalinsa bayan yan bindiga sun bindige shi yayin da ya je kada kuri’a a yankin Anyigba, a karamar hukumar Dekina, Kogi.
Akalla mutum 15 yan sanda suka kama kan zargin samunsu da kwamfutocin laftof da manhajojin da za a yi amfani da su wajen yin kutse a sakamakon zabe a Katsina.
Zaben Shugaban kasan Najeriya
Samu kari