Ana Zargin Bola Tinubu Ya Hada Baki da Gwamnan PDP, Zai Sauya Sheka Bayan Zabe

Ana Zargin Bola Tinubu Ya Hada Baki da Gwamnan PDP, Zai Sauya Sheka Bayan Zabe

  • Jita-jita na yawo cewa bayan zabe, Seyi Makinde zai sauya-sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC
  • Ana zargin Gwamnan jihar Oyo ya yi wa APC aiki a boye a zaben Shugaban kasa duk da yana PDP
  • Wani ‘dan kwamitin takarar APC ya ce babu wata yarjejeniya tsakanin Bola Tinubu da Makinde

Oyo - Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya ce babu wata yarjejeniya da ya ajiye da Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde.

Hukumar dillacin labarai na kasa ta rahoto kwamitin yakin takaran APC ya ce game da zabukan jihar Oyo, ba a shiga wata yarjejeniya da Gwamna ba.

Nike Ajagbe wanda tana cikin ‘yan kwamitin ya shaidawa manema labarai wannan a wata hira.

Hakan na zuwa ne bayan rade-radi sun fara yawo daga wani zama da fusatattun ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP na reshen jihar Oyo suka yi a makon nan.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnoni: Buhari Ya Bada Hakuri Kan Canjin Kudi, Ya Bayyana ‘Yan Takaransa

Tinubu ba zai yaudari APC ba

A cewarta, Bola Tinubu cikakken ‘dan jam’iyya ne saboda haka ba zai sadaukar da nasarar ‘yan takaransu na APC a Oyo saboda ya lashe zabensa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

NAN ta rahoto ‘dan siyasar yana cewa babu dalilin da Tinubu zai yi wasa da nasarar 'ya 'yan APC musamman a yankin da ya fito na Kudu maso yamma.

Bola Tinubu
Bola Tinubu a gidan Gwamnatin Oyo Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

A madadin kwamitin PCC, Ajagbe ta ce mutane su daina tunanin saboda Makinde da ‘dan takaransu sun hadu, shikenan ana marawa tazarcensa baya.

Jawabin Nike Ajagbe

"Yana cikin tsare-tsaren kwamitin yakin neman zabe ziyartar Gwamnonin jihohin adawa a duk inda suke domin yin kamfe.
Ziyarar da aka kai ba ta da wata alaka da tallata Gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde."

- Nike Ajagbe

Seyi Makinde zai sauya-sheka?

PM News ta ce ana jita-jita cewa Mai girma Seyi Makinde ya shaidawa ‘yan takaran PDP da suka sha kashi a zaben majalisar tarayya cewa zai bar PDP.

Kara karanta wannan

Bayan Tinubu Ya Ci Zaɓe, Babban Jigon PDP Ya Jingine Tafiyar Atiku, Ya Koma Jam'iyyar APC

Idan wannan labari ya tabbata, da zarar Bola Tinubu ya zama shugaban kasa, kuma Makinde ya samu tazarce a jihar Oyo, zai fice daga PDP zuwa APC.

Kungiyar YIAGA na zargin an murde zabe

Ku na da labari cewa hasashen da Kungiyar YIAGA tayi ya nuna akwai ta-cewa game da sakamakon zaben 2023 da Bola Tinubu ya doke PDP da LP.

Hukumar INEC ta bada sanarwar cewa ‘Dan takaran APC watau Bola Tinubu ya samu kuri’u 231, 591 a jihar Ribas, YIAGA ta ce da alama an yi magudin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel