Shugaban APC Na Ƙasa Ya Caccaki Jam'iyyun PDP Da Labour Party

Shugaban APC Na Ƙasa Ya Caccaki Jam'iyyun PDP Da Labour Party

  • Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya caccaki jam'iyyun adawar ƙasar nan
  • Abdullahi Adamu yace jam'iyyun suna ƙoƙarin shafawa nasarar da jam'iyyar sa ta samu baƙin fenti a idon ƴan Najeriya
  • Ya kuma shawarce su kan su bi hanyoyin da ya dace wajen neman haƙƙin su idan suna ganin ba ayi musu daidai ba

Abuja- Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Abdullahi Adamu, yace jam'iyyun PDP da Labour Party, so suke su sanya nasasar da jam'iyyar sa ta samu tayi baƙin jini a idon ƴan Najeriya. Rahoton The Cable

Yayin da yake tattaunawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis, Abdullahi Adamu, yace abin kunya ne halayyar da jam'iyyun suka nuna a ƙoƙarin su na jefa ƙasar nan cikin ruɗani.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Wasu Abubuwa 5 Da Suka Taimaka Wajen Samun Rashin Nasarar Rabiu Kwankwaso

Abdullahi Adamu
Shugaban APC Na Ƙasa Ya Caccaki Jam'iyyun PDP Da Labour Party Hoto: The Cable
Asali: UGC
"Ficewar da suka yi daga wajen tattara sakamakon zaɓe ma ƙasa yarinta ce, kuma sun yi hakan ne domin nuna raini ga hukumar zaɓe." A cewar Adamu
“Kiran da suka yi na a soke zaɓe kan wasu zarge-zarge marasa tushe ballantana makama ya nuna ƙurewar su wajen neman mulki ido rufe."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Dole ne dukkanin masu kishin ƙasar nan waɗanda ke son zaman lafiya da haɗin kai su yi magana da murya ɗaya wajen wajen yin Allah wadai da waɗannan mutanen waɗanda suke suke son nuna kan su a matsayin mutanen kirki."

Adamu yace babu wani waje a kundin tsarin mulki da ya basu damar su yi watsi da abinda ƴan Najeriya suke so.

“Mulki a hannun mutane yake sannan dole ne a bar su suyi amfani da shi yadda ya dace wajen zaɓar shugabannin da suke so..

Kara karanta wannan

Da Zafi Zafi: Jam'iyyun PDP, LP, ADC Sun Buƙaci Shugaban INEC yayi Murabus Tare Da Sake Sabon Zaɓe

“Dokokin mu sun samar da hurumin neman bin kadi kan zaɓe. Muna kira ga dukkanin waɗanda suke ganin anyi musu ba daidai ba, da su bi hanyoyin da ya dace wajen neman haƙƙin su."

A ranar Talata ne dai jam'iyyun adawa suka nemi hukumar INEC da ta sake sabon zaɓe, sannan suka nuna rashin goyon bayan su ga shugabancin hukumar na Farfesa Mahmood Yakubu. Rahoton Premium Times

Kwamishina Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa Kwana 10 Gabanin Zaben Gwamnoni

A wani rahoton kuma, wani kwamishina yayi murabus daga muƙamin sa ana saura kwana goma a yi zaɓen gwamnoni.

Hakan dai ba ƙaramar barazana bace ga gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel