Abin da Ya Faru da ‘Yan Gidan Manya 13 da Suka Nemi Takarar Majalisar Tarayya

Abin da Ya Faru da ‘Yan Gidan Manya 13 da Suka Nemi Takarar Majalisar Tarayya

  • Wasu daga cikin ‘ya ‘yan manyan Najeriya sun nemi kujerun majalisar tarayya a zaben shekarar nan
  • Wadannan ‘yan takara sun karawa zaben bana armashi, a karshe wasu daga cikinsu sun samu nasara
  • A rahoton nan, mun tattaro sakamakon zaben da ‘ya ‘yan manyan shugabannin kasar nan suka shiga

1. Bello El-Rufai

A takarar farko da ya shiga a siyasa, Bello El-Rufai ya yi galaba a kan Hon. Samaila Suleiman, ya hana ‘dan majalisar mai-ci sake zarcewa karo na uku a PDP.

Yaron Gwamnan Kaduna ya samu kuri’u 51,052 a jam’iyyar APC. ‘Dan takaran PDP ya zo da na biyu da 34,808 a kujerar Kaduna ta Arewa a majalisar wakilai.

2. Abba Ganduje

A zaben da aka shirya a makon da ya gabata, Umar Abdullahi Ganduje bai yi nasara wajen zama ‘dan majalisa mai wakiltar Dawakin Tofa- Tofa da Rimin Gado ba.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Tona Wadanda Suka Fatattaki Peter Obi Daga Jam’iyyar PDP Daf da Zabe

Honarabul Tijjani Abudlkadir Jobe da ya yi takara a NNPP ya doke ‘dan Gwamnan jihar Kano. ‘Dan majalisar ya samu kuri’u 52, 456, Abba ya tashi da 44,809.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

3. Joshua Gana

A jam’iyyar PDP ne yaron Farfesa Jerry Gana watau Joshua ya yi galaba a zaben ‘dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabun Lavun/Mokwa/Edati da ke jihar Neja.

Yaron tsohon Ministan yada labaran kasar ya samu kuri’u 47, 942 wajen hana Hon. Abdullahi Usman Gbatamangi da ya samu kuri’u 40, 002 komawa majalisa.

4. Jide Obanikoro

Babajide Obanikoro ba zai je majalisar wakilai ba a dalilin nasarar da Thaddeus Attah ya samu a karkashin jam’iyyar LP a zaben yankin Eti-Osa da ke jihar Legas.

Attah ya doke Obanikoro wanda mahaifinsa ya rike Sanata da Minista. LP ta hana Obanikoro zarcewa a karo na biyu, sannan ta takawa mawaki Banky W burki.

Kara karanta wannan

A gudu tare: Tinubu ya kafa kwamitin sulhu da su Atiku, gwamnan APC ya fadi dalili

5. Sadiq Ango Abdullahi

An samu canjin ‘dan majalisar tarayya daga mazabar Sabon Gari a jihar Kaduna. Sadiq Ango Abdullahi na PDP zai canji Garba Datti Muhammad na jam’iyyar APC.

‘Dan takaran na PDP watau Sadiq Ango Abdullahi ‘da ne ga Farfesa Ango Abdullahi, sannan mahaifiyarsa ita ce Marigayiya Aisha Jummai Alhassan (Mama Taraba).

Bello El-Rufai
Bello El-Rufai Hoto: Bello El-Rufai House of Reps.
Asali: Facebook

6. Blessing Onuh

Duk da yana cikin jagororin jam’iyyar adawa ta PDP, diyar David Mark tayi takara a jam’iyyar APC a jihar Benuwai, kuma tayi galaba a kan Hon. Alex Ogbe na PDP.

Blessing Onuh ta lashe zaben majalisa na mazabar Otukpo/Ohimini da kuri’u 29, 031. Wanda ya zo na biyu a yankin na jihar Benuwai a zaben ya samu kuri’u 21,742.

7. Ibrahim Bello Mohammed

Wanda zai zama ‘dan majalisar Birnin-Kebbi, Kalgo da Bunza daga 1 ga watan Yunin 2023 shi ne Alhaji Ibrahim Bello Mohammed mai shekara 27 da haihuwa.

Ba a banza Ibrahim Bello Mohammed wanda aka fi sani da IBM ya yi nasara ba, mahaifinsa, Dr. Bello Mohammed Haliru ya taba rike shugabancin PDP na kasa.

Kara karanta wannan

Wasu Abubuwa 5 da Suka Taimakawa Bola Tinubu Wajen Samun Nasara a Zaben 2023

8. Erhiatake Ibori-Suenu

Erhiatake Ibori-Suenu ta lashe kujerar Ethiope a majalisar tarayya. Diyar tsohon Gwamnan Delta, James Ibori ta shiga takara a PDP, ta lallasa Halims Agoda na APC.

9. Abdussamad Dasuki

Kwamishina a gwamnatin Aminu Tambuwal, Abdussamad Dasuki zai koma majalisa domin wakiltar mutanen Kebbe/Tambuwal bayan nasararsa a PDP.

Hon. Abdussamad Dasuki 'dan gidan Sarkin Musulmi, Alhaji Ibrahim Dasuki ne.

10. Mai dakin Akume

Zaben 2023 ya kawo Regina Akume a matsayin ‘yar majalisar Tarka/Gboko. Tsohuwar uwargidar jihar Benuwan ta ci zabe a APC, tayi galaba kan John Dyeh.

Matar Ministan harkokin musamman ta samu kuri’u 47,086, PDP mai 24, 639 ta zo na biyu a takarar. Mai gidanta ya yi Minista kafin ya rasa tazarce a zaben 2019.

11. Chinedu Orji

Rt. Hon. Chinedu Orji ba zai je majalisar wakilai ba domin ya sha kashi a takarar Ikwuano/Umuahia. ‘Dan takaran LP ya doke PDP da ratar kuri’u 13, 000.

Mahaifin shugaban majalisar dokokin, Thedore Orji ya yi gwamna na shekaru takwas a Abia.

Kara karanta wannan

INEC Ta Ayyana Shekarau da Ya Koma PDP a Matsayin Wanda Ya Ci Zaben Sanata a NNPP

12. Abdulaziz Yaradua

Kanin tsohon Shugaban Najeriya, Kanal Abdulaziz Yaradua zai zama Sanatan Katsina ta tsakiya. Tsohon sojan ya lashe zabe a jam’iyyar APC, ya bi layin gidansu.

Atiku zai koma kotu

Lauyoyin da sun kai matsayin SAN su na shirin da zai hana Jam’iyyar APC cigaba da rike kasa. An ji labari masana shari’an za su je kotu domin kare PDP.

Kakakin kwamitin yakin neman zaben PDP ya ce akwai Lauyoyi da za su yi aiki ko babu kudi domin ganin Atiku Abubakar ya samu shugabancin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel