Atiku Ya Tona Wadanda Suka Fatattaki Peter Obi Daga Jam’iyyar PDP Daf da Zabe

Atiku Ya Tona Wadanda Suka Fatattaki Peter Obi Daga Jam’iyyar PDP Daf da Zabe

  • Atiku Abubakar ya ce Gwamnoni suka tsorata Peter Obi, suka yi sanadiyyar ficewarsa daga PDP
  • ‘Dan takaran Shugaban kasar na jam’iyyar PDP ya nuna Obi ya karaya kafin zaben tsaida gwani
  • Wazirin Adamawa bai tsorata da Gwamnonin ba, ya samu takara amma LP tayi masa illa a zabe

Abuja - Atiku Abubakar ya yi magana a kan abubuwan da suke je suka dawo, har jam’iyyar PDP tayi asarar Peter Obi zuwa LP gabanin zaben 2023.

A ranar Alhamis Vanguard ta rahoto Alhaji Atiku Abubakar yana cewa Gwamnonin jihohin adawa suka dage cewa su za a ba tikitin PDP a zaben bana.

‘Dan takaran ya yi wannan bayani ne da yake zantawa da manema labarai game da matakin da za su dauka a game da takarar da ya rasa a makon jiya.

Kara karanta wannan

A gudu tare: Tinubu ya kafa kwamitin sulhu da su Atiku, gwamnan APC ya fadi dalili

Wazirin Adamawa ya ce garaje ya yi wa Peter Obi yawa, a karshe ya balle ya nemi takara a LP, sauya shekarsa ta jawo aka raba kuri’un ‘yan adawa.

Gwamnonin PDP sun tsora Obi

Kamar yadda Atiku Abubakar ya shaidawa ‘yan jarida, bukatun da Gwamnonin PDP suka zo da shi, ya tsorata tsohon Gwamnan Anambra ya koma LP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

‘Dan takaran ya yarda cewa rasa kuri’un Kudu maso gabas da kuri’un Kudu maso kudu da PDP tayi, ya jawo duk suka rasa kujerar shugabancin kasa.

Atiku
Atiku, Ayu da Okowa a taron PDP Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

An rahoto tsohon mataimakin shugaban na Najeriya yana mai cewa da ya samu mulki, zai yi wa mutanen Ibo saukin darewa kan kujerar shugaban kasa.

“Ina tunanin gaggawa tayi wa Peter Obi yawa. Da muka fara kamfe, sai Gwamnoninmu na PDP suka ce dole su fito da shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Atiku da Peter Obi Sun Ki Sallamawa Bola Tinubu, Sun Fadi Matsayar da Za Su Dauka

Su kace a cikinsu za a samu mataimakin shugaban kasa da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Peter ya tsorata, ya sauya-sheka.
Ban ji tsoro ba, na yi takara da Gwamnonin. Lokacin da muka kafa PDP, watakila wasunsu su na makarantar sakandare ko kuwa jami’a.

Da na sani, keya ce

Me zai sa in tsorata, na gwabza da su, na lashe zaben fitar da gwani. Da ya zauna, da babu wani abin da zai hana shi zama abokin takarata.
Gaskiya kusan ya yi wa PDP illa, domin duk kuri’un da ya kamata su tafi ga PDP a Kudu maso gabas Kudu maso kudu sun tafi wajensa."

- Atiku Abubakar

Makinde zai bi Tinubu?

Ku na sane cewa Gwamnan Oyo yana cikin ‘Yan tawagar G5 da suka yi fada da Atiku Abubakar a Jam’iyyar PDP, a karshe aka yi haihuwar guzuma.

Yanzu ana batun Gwamna Seyi Makinde zai sauya-sheka zuwa APC idan an rantsar da Bola Tinubu, rahoto ya zo cewa APC PCC ya musanya zancen.

Kara karanta wannan

Na Hannun Dama Ya Ba Tinubu Shawara Ya Jawo Kwankwaso da Peter Obi a Gwamnati

Asali: Legit.ng

Online view pixel