A Shirye Muke Mu Hadu a Kotu, APC Ta Mayar Wa Obi Martani Mai Zafi

A Shirye Muke Mu Hadu a Kotu, APC Ta Mayar Wa Obi Martani Mai Zafi

  • Jam’iyyar APC ta ce ba ta tsoron abin da zai biyo baya a kotu a batutuwan da Peter Obi ya yi a ranar Alhamis
  • Peter Obi ya ce shi ne ya lashe zaben shugaban kasa na ranar Asabar, amma aka kwace aka ba Bola Tinubu
  • A bangare guda, jam’iyyar APC ta ce ta kafa kwamitin da zai tattauna da dukkan ‘yan takarar da suka yi takara bana

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC mai mulkin kasa ta bayyana cewa, a shirye take ta hadu dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Peter Obi kan kalubalantar sakamakon zabe da yace zai yi.

Bayan zaben shugaban kasa na ranar Asabar, Bola Ahmad Tinubu ya ci zabe, lamarin da ya fusata Obi da sauran ‘yan takara a kasar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: "Ta Tabbata Tinubu Ne Zabin Yan Najeriya" Shugaban APC Ya Yi Magana Mai Jan Hankali

Ob ya bayyana cewa, zai dauki matakin doka tare da kalubalantar sakamakon zaben da INEC tace Tinubu ne ya lashe zabe.

A shirye muke mu gamu a kotu, APC ga Obi
Bola Tinubu na APC (Hagu) da Peter Obi na LP (Dama) | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

A martaninta ga batun Obi, jam’iyyar mai mulki ta ce mai tsoro ka fasa, kawai a hade a kotu tsakanin Obi da Tinubu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An sace mana nasararmu ne a zaben nan, inji Obi

A baya Obi ya bayyana cewa, shi ne ya samu nasara a zaben da aka yi, kawai an sace masa nasarar ne ta hanyar ba Tinubu takardun shaidar lashe zabe.

Hakazalika, jam’iyyar ta bayyana cewa, ta ga lam’a da yawa da maganganun Obi na ranar Alhamis, inda ya fadi maganganu masu yawa kan zaben bana.

A gefe guda, APC ta ce, ya kamata kafin ma Obi ya tafi ita ta fara maka shi, domin kuwa akwai bukatar kalubalantar ikrarinsa da yawa.

Kara karanta wannan

Shikenan: Jigon PDP ya tono gaskiyar dalilin da yasa Obi ya fi Tinubu kuri'u a jihar Legas

Zaben bana ne zabe mafi nagarta

Jam’iyyar APC ta kuma bayyana cewa, ta gamsu da yadda aka yi gaskiya da zabe mai nagarta a Najeriya a wannan karon, TheEagle tattaro.

A cewarta, wannan ne zabe mafi nagarta da aminci da aka yi a Najeriya, kuma abin a yabawa hukumar zabe da gwamnatin APC ne.

Peter Obi dai na da ra’ayin cewa, ‘yan Najeriya, musamman matasa na kaunarsa, kuma sun bashi kuri’un da zai daura shi a kujerar Buhari.

An kafa kwamitin tattaunawa da su Atiku da Obi

A gefe guda, jam’iyyar APC ta bayyana cewa, tuni Tinubu ya kafa kwamitin da zai tattauna da Atiku da Obi.

Wannan na zuwa ne bayan da aka ayyana Tinubu a matsayin zababben shugaban kasan Najeriya a zaben bana.

Har yanzu ana ci gaba da aiko da sakwannin taya murna ga Tinubu bayan ya lashe zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel