Ni Na Lashe Zaben Shugaban Kasa Kuma Zan Tabbatar da Haka, Obi

Ni Na Lashe Zaben Shugaban Kasa Kuma Zan Tabbatar da Haka, Obi

  • Mista Peter Obi ya lashi takobin kalubalantar zaben shugaban kasan da aka kammala a Kotu
  • Ɗan takarar shugaban kasa na LP ya ce ko tantama babu shi ne ya lashe zaben amma aka masa karfa karfa
  • INEC ta ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya samu naaara da kuri'u mafi rinjaye

Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party a zaben da aka kammala, Peter Obi, ya ce shi ne ya samu nasara a zaben ranar Asabar da ta gabata kuma zai tabbatar da hakan.

Daily Trust ta rahoto cewa Mista Obi ya yi wannan ikirarin ne ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja a wurin taron manema labarai, wanda ya raɗa wa martanin farko.

Peter Obi.
Peter Obi yayin da yake jawabi na farko bayan faɗuwa zabe Hoto: Peter Obi
Asali: Twitter

Obi ya ce zaben da aka kammala ya yi kama da fashin tsakar rana ido na gani ido kuma zai bi duk wata hanya da doka ta tanada, ciki har da zuwa Kotu don kwato haƙƙinsu da aka kwace shi da Datti Baba Ahmed.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito, An Bayyana Gwamnan PDP Da Ya Taimaka Aka Kayar da Atiku Ranar Zabe

Tsohon gwamnan jihar Anambran ya ƙara da cewa ya yi amanna bangaren shari'a zai masa adalci, inda ya kara da cewa, "Ina daga cikin waɗanda suka amfana da shari'a."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa ya garzaya Kotu lokuta da dama domin kwato haƙƙinsa da aka kwace kuma ya samu nasara baki ɗaya.

Bugu da ƙari ya ce ganawar da suka yi da jam'iyyar PDP da wasu jam'iyyun siyasa ba ta Maja bace, sun zauna ne domin tattaunawa da musayar ra'ayi kan matakin da zasu ɗauka na gaba.

"Zan kalubanci matakan da aka bi wajen gudanar da zaɓe, babu adalci a ciki, mutane basu yi tsammanin haka ba," inji Obi, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Gabanin fara taron yan jaridan, Obi ya yi shirun minti guda domin karrama waɗanda suka ji raunuka da waɗanda suka rasa rayukansu ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Bayan Tinubu Ya Ci Zaɓe, Babban Jigon PDP Ya Jingine Tafiyar Atiku, Ya Koma Jam'iyyar APC

Kwamishina ya yi murabus a Gombe

A wani labarin kuma Kwamishina Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa Kwana 10 Gabanin Zaben Gwamnoni

Kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Gombe ya yi ikirarin cewa an naɗa kan muƙamin ne a takarda kaɗai amma babu abinda yake samu don taimakon mutane.

A wata takarda da ta bayyana kwamshinan ya gode wa gwamna Inuwa Yahaya kana ya sanar da aje aikinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel