Firaministan Ingila Ya Taya Tinubu Murnar Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa

Firaministan Ingila Ya Taya Tinubu Murnar Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa

  • Firaministan Ingila yabi sahun dubun dubatar masu aikewa da saƙon taya murna ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya
  • Rishi Sunak ya bayyana shirin da Ingila take da shi domin yin aiki hannu da hannu da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar
  • Bola Tinubu ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya bayan ya doke sauran abokan takarar sa

Firaministan Ingila, Rishi Sunak, ya taya zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya, Bola Tinubu, murnar lashe zaɓen shugaba ƙasa da yayi. Rahoton Channels Tv

Ƙasashen Ingila da Najeriya suna da dangantaka mai kyau wacce ta shafe sama da shekara 62, tun daga lokacin da Najeriya ta samu ƴancin kanta daga Ingila.

Tinubu da Rishi Sunak
Firaministan Ingila Ya Taya Tinubu Murnar Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wani rubutu da firaministan na Ingila yayi a shafin sa na Twitter, ya jaddada shirin sa na ganin ya ba zaɓaɓɓen shugaban ƙasar dukkanin goyon bayan da yakamata domin ƙara ƙarfafa dangantakar dake a tsakanin su.

Kara karanta wannan

Zaɓukan 2023: Tinubu ya Aikawa Atiku da Obi Ƙwaƙwƙwaran Saƙo Bayan INEC Ta Ayyana Shi a Matsayin Mai Nasara

A kalamansa:

“Ina taya @officialABAT murna kan nasarar da ya samu a Najeriya. Dangantakar dake tsakanin ƙasashen Ingila da Najeriya, mai ƙarfi ce."
"A shirye nake da muyi aiki tare domin ƙara bunƙasa alaƙar tsaro da kasuwancin mu, samar da sababbin damarmaki na yin kasuwanci da kawo cigaba a kasashen mu baki ɗaya."

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a ranar Laraba.

Bayan an fafata sosai a tsakanin ƴan takarar a zaɓen ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu, Tinubu mai shekara 70 a duniya, wanda yayi takara a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya lashe zaɓen.

Tinubu ya lashe zaɓen ne da ƙuri'u 8,794,726, inda ya ba wanda ya zo na biyu a zaɓen, Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tazarar kusan ƙuri'u miliyan biyu.

Tsohon Shugaban Kasa, Janar Babangida Ya Fito Ya Yi Maganar Zabe da Nasarar Tinubu

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Wasu Abubuwa 5 Da Suka Taimaka Wajen Samun Rashin Nasarar Rabiu Kwankwaso

A wani labarin na daban kuma, tsohon shugaban ƙasa Ibrahim Badamasi Babangida, ya fito yayi magana kan zaɓen Najeriya da nasarar da Bola Tinubu ya samu a zaɓen.

Janar Babangida ya yaba kan yadda INEC ta gudanar da zaɓen na bana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel