Hukumar EFCC
Oba na Benin, Ewuare II ya zargi hukumar yaki da cin hanci ta EFCC inda ya ce wasu jami'anta na karbar rashawa musamman fifita wadanda suka fi bata kuɗi.
‘Dan kwangila ya tona yadda ya ba da cin hancin $600, 00 a lokacin Godwin Emefiele. Victor Onyejiuwa ya kashe $600, 000 (kusan N300m) kafin hakkokinsa su fito a CBN.
Dan Najeriya ya saci wasu adadi na kudaden da suka kai $22,000 a Amurka, EFCC ta gaggauta daukar kudin tare da mikawa hukumar tsaron Amurka ta FBI.
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya ce wasu matasa da ke harkar crypto ba su san ana amfani da su wajen daukar nauyin ayyukan ta’addanci a Najeriya ba.
Babbar kotun Abuja ta yi fatali da buƙatar tsohon ministan wuta, Olu Agunloye na dakatar da shari'ar da ake masa kan yadda aka batar da kuɗin kwangilar Mambilla.
Hukumar hana yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) ta bayar da tabbacin cewa sannu a hankali ta ke ci gaba da bincikar Bello Matawalle.
Babbar kotun tarayya mai zama a Maitama a Abuja ta amince da ba da belin tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele bayan ya musanta laifukan da ake tuhumarsa.
EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele bisa zargin badakala. Bayan sauraron karar, kotun ta bada belinsa a yau.
Rahotan da ke nuna cewa hukumar EFCC tana neman Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ruwa a jallo ba gaskiya bane, kamar yadda sahihin bincike ya nuna.
Hukumar EFCC
Samu kari