Emefiele: “Yadda Na Biya Cin Hancin $600, 000 Domin a Biya Ni Kudin Kwangila a CBN”

Emefiele: “Yadda Na Biya Cin Hancin $600, 000 Domin a Biya Ni Kudin Kwangila a CBN”

  • Victor Onyejiuwa ya ce sai da ya biya rashawa kafin wasu kudin kwangilar da ya yi a bankin CBN a shekarun baya ya fito
  • ‘Dan kasuwan ya yi wannan fallasa ne da aka gayyato shi a matsayin wanda zai ba da shaida a gaban kotu mai zama a Legas
  • Idan maganar Onyejiuwa ta tabbata, sai da ya kashe $600, 000 (kusan N300m a lokacin) kafin a biya shi gumin da ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Lagos - Wani ‘dan kwangila a CBN, Victor Onyejiuwa ya shaidawa kotu yadda ya biya cin hanci ga shugabannin babban bankin kasar.

Victor Onyejiuwa ya yi wannan bayani ne a kotun laifuffuka na musamman da ke zama a birnin Ikeja da ke jihar Legas a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Wike v Fubara, Ganduje v Abba da wasu manyan gwabzawar da ake jira a 2027

Godwin Emefiele
Godwin Emefiele a lokacin yana bankin CBN a Abuja Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

'Dan kwangila ya biya rashawa lokacin Emefiele

‘Dan kwangilar ya ce an bukaci ya biya rashawar $600, 000 kafin kudin kwangilolin da ya yi a CBN su fito, kuma ya ba John Ayoh kudin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Punch ta ce John Ayoh ya taba rike Darektan sashen kimiyyar sadarwa na zamani a CBN.

CBN: An kira 'dan kwangila ya ba da shaida

Onyejiuwa ya yi wannan bayani a matsayin wanda aka kira ya ba da shaida a shari’ar da ake yi da tsohon gwamna Godwin Emefiele.

A cewar Onyejiuwa, duk wata tattanawa da aka yi ta kasance ta manhajar WhatsApp.

Cin hanci da rashawar $600, 000 a CBN

Leadership ta ce shaidan ya yi ikirarin ya biya $400,000 a Legas daga nan ya aika sahu na biyu na kudin watau $200,000 a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Jama’a Sun Soki Shirin Tinubu Na Kashe Naira Tiriliyan 20 da Aka Ajiyewa ‘Yan Fansho

A jawabin da ya yi wa kotu, Onyejiuwa ya ce shugabannin CBN ba su rubuto masa da takarda da ke umartar ya biya cin hancin ba.

Olalekan Ojo, SAN shi ne lauyan gwamnati da ya rika yi wa Onyejiuwa tambayoyi a kotun.

Kwangiloli babu cin hanci a bankin CBN

Onyejiuwa yake cewa ko bayan Ayoh ya bar bankin a 2019, ya cigaba da yin kwangiloli, kuma an biya shi ba tare da cin hanci ba.

Shi dai Onyejiuwa ya ce bai aikata laifuffukan da ake tuhumarsa da su a shari’ar da ake yi da Godwin Emefiele da Mista Henry Omoile ba.

CBN tana fama da Naira a kasuwa

A baya kun samu labari cewa watakila Dalolin da Yemi Micheal Cordoso ya rabawa ‘yan canji ya rage karancin kudin kasashen ketare.

Bayanai sun tabbatar da Naira ta mike kadan duk da kashin da ta tashi a hannun Dala, sai dai daga baya kudin Najeriyan ya karye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel