Crypto: EFCC Ta Gano Hanyar da Masu Daukar Nauyin Ta’addanci Ke Hada Hadar Kudi

Crypto: EFCC Ta Gano Hanyar da Masu Daukar Nauyin Ta’addanci Ke Hada Hadar Kudi

  • Hukumar EFCC ta ce ana amfani da wasu matasa da ke kasuwancin crypto wajen daukar nauyin ayyukan ta’addanci a Najeriya ba
  • Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce 'yan ta'addan na amfani da irin su Binance wajen yin hada-hadar kudaden ayyukan ta’addanci
  • Olukoyede ya ce akwai bukatar a yi amfani da fasaha wajen bin diddigin kudaden da ake amfani da su wajen aikata laifuffuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar EFCC ta bayyana cewa ‘yan ta’adda na amfani da Binance da sauran manhajojin cryptocurrency wajen samar da kudin da suke daukar nauyin ta'addanci a Nigeria.

EFCC ta yi magana kan masu daukar nauyin ta'addanci
EFCC ta ce ana amfani da kasuwannin crypto wajen daukar nauyin ta’addanci a Nigeria. Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

Amfani da 'yan crypto a ayyukan ta'addanci

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce 'yan ta'addan na amfani da matasa da ke harkar crypto wajen hada-hadar kudin ba tare da sun san duhun garin ba.

Kara karanta wannan

"An yi amfani da bam": Mutum 1 ya mutu da aka bankawa masallata wuta a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Olukoyede ya yi magana ne a ranar Laraba a taron masu ruwa da tsaki kan yaki da safarar kudi domin daukar nauyin ta'addanci.

Shugaban hukumar ta EFCC ya ce wasu daga cikin matasan da ke karbar kudi domin yin kasuwanci na crypto ba su san cewa masu kudin su ne ke daukar nauyin ta’addanci ba.

Ya kara da cewa wasu daga cikin asusun banki 1,146 da hukumar yaki da cin hanci da rashawar ta rufe su a baya-bayan nan, na masu daukar nauyin ta'addanci ne.

Ana daukar nauyin ta'addanci ta hanyar crypto

A cewar Olukoyede:

"Ana amfani da kasuwannin crypto wajen daukar nauyin ta'addanci. Abubuwan da muka gano a bincikenmu kan ire-iren wadannan kasuwannin abin tayar da hankali ne.
"Mun yi tunanin Binance ce babba a ciki, amma daga bisani muka gano akwai wadanda ayyukansu ya wuce hankali.

Kara karanta wannan

Tinubu ya haramtawa mukarraban gwamnati sayen motocin da suka dogara da fetur

“Suna yin amfani da wasu daga cikin wadannan matasan masu yin crypto. Matasan ba su da masaniyar masu ba su kudin na daukar nauyin ta'addanci ne da kudin.

EFCC za ta fara bibiyar kudaden ta'addanci

Shugaban EFCC ya ce akwai bukatar a yi amfani da fasaha wajen bin diddigin kudi da ake amfani da su wajen daukar nauyin ayyukan ta’addanci a kasar nan, in ji rahoton The Cable.

Olukoyede ya ba da labarin yadda wani abokinsa a hukumar FBI ta Amurka ya sanar da shi cewa ana iya bin diddigin kudaden dala a fadin duniya ta hanyar fasaha.

"Yana da mahimmanci a gare mu mu rungumi amfani da irin wannan fasahar."

- Ola Olukoyede.

An ci tarar Binance Dala biliyan 10

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Nigeria, ta nemi diyyar Dala biliyan 10 daga kamfanin hada-hadar kudaden crypto na Binance.

Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasar shawara ta fuskar yada labarai ya ce an ci Binance tarar ne saboda karya dokokin cinikayya na kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.