Ba a Gama da Obi Cubana Ba, EFCC Ta Cafke Wata ’Yar Arewa Kan Watsa Takardar Naira

Ba a Gama da Obi Cubana Ba, EFCC Ta Cafke Wata ’Yar Arewa Kan Watsa Takardar Naira

  • Masu bincike na shiyyar Gombe a hukumar EFCC sun kama Janty Emmanuel bisa zargin cin zarafin kudin Najeriya a Gombe
  • An kama ta ne a ranar Litinin, 20 ga Mayu, 2024 biyo bayan bayanan sirri da suka nuna ta na watsa takardun Naira a wani taron biki
  • Bayan kama wanda ake zargin, an nuna mata bidiyon inda take rawa a G-Connect, Tumfure, jihar Gombe, kuma ta amsa laifinta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Gombe - Hukumar EFCC ta ce jami’anta a Gombe sun kama wata mata mai suna Janty Emmanuel da laifin cin zarafin Naira a wajen wani taron biki.

Hukumar EFCC ta ce an kama Emmanuel ne a ranar Litinin bayan an ganta a faifan bidiyo tana watsa takardar Naira a wajen taron.

Kara karanta wannan

NDLEA ta fara farautar miji da mata kan safarar hodar iblis tsakanin Indiya da Najeriya

EFCC ta kama mai cin zarafin kudin Najeriya a Gombe
EFCC ta kama matashiya 'yar Gombe bisa zargin cin zarafin kudin Najeriya. Hoto: officialefcc
Asali: Facebook

Kakakin hukumar, Dele Oyewale, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a shafin hukumar na Facebook a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC: Matashiyar ta amince da aikata laifin

Dele Oyewale ya ce Emmanuel ta amince da aikata laifin da ake tuhumarta bayan an nuna mata wata hujja ta faifan bidiyo.

Kakakin hukumar EFCC ya kara da cewa za a gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike kan lamarin.

“Bayan kama wadda ake zargin, an nuna mata bidiyon inda take rawa a G-Connect, Tumfure, a jihar Gombe, ta na kuma watsa takardun Naira 'yan dubu dubu.
“Ta amince da aikata laifin. Za a gurfanar da ita gaban kotu da zarar an kammala bincike.”

- Dele Oyewale.

A ranar Litinin ne hukumar ta sanar da cewa ta kama wasu mutane 31 da ke da hannu wajen hada-hadar kudi ba bisa ka'ida ba da kuma cin zarafin Naira a Kano.

Kara karanta wannan

An kame satasan da suka yi amfani da bindigar sasan yara wajen Sace mota a Enugu

EFCC ta gurfanar da Obi Cubana

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar EFCC ta gurfanar da wani dan kasuwa, Pascal Okechukwu, wanda aka fi sani da Cubana Chief Priest, a kan tuhume-tuhume uku.

Okechukwu dai na fuskantar tuhume-tuhume da suka shafi watsa takardun Naira a wajen wani taron biki wanda ya saba wa dokar babban bankin kasar ta 2007.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.