Hukumar EFCC
Hukumar EFCC ta bayyana sababbin hanyoyi da 'yan yahoo suka kirkiro domin damfarar mutane. Babban daraktan hukumar ne Effa Okim ya bayyana haka a jihar Edo.
Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta yi watsi da bukatar da Yahaya Bello ya gabatar wanda ya nemi a dakatar da shari'ar da ake masa kan karkatar da N80bn.
Ana so sanatoci su kawo doka a majalisa da za ta aika duk wanda ya saci dukiyar kasa watau gwamnati ya sheka barzahu kamar yadda ake harin masu harkar kwaya.
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya amince zai miƙa kansa domin fuskantar shari'a a babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ranar 13 ga watan Yuni.
Babbar kotun tarayya ta fusta kan yadda Yahaya yake ci gaba da kin bayyana a gabanta. Mai shari’a Emeka Nwite ya yi fataki da bukatar hana EFCC kama Bello.
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya bayyana a gaban kotu kan zargin badaƙalar N7.2bn. Sirika ya yi magana kan yiwuwar tafiya gidan kurkuku.
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika, ɗiyarsa, da wasu mutane biyu kan N100m kowanne.
Binciken gano gaskiya da aka gudanar kan hoton da ake yaɗawa cewa Yahaya Bello ya yi shigar ƴan Daudu ya gano cewa ba tsohon gwamnan bane a hoton.
Hukumar EFCC ta tabbatar da cewa za ta gurfanar da tsohon Ministan Buhari, Hadi Sirika a gaban kotu a gobe Alhamis 9 ga watan Mayu kan zargin wawushe N2.7bn.
Hukumar EFCC
Samu kari