Badaƙalar $6bn: Tsohon Ministan Wutar Lantarki Ya Gamu da Babbar Matsala a Kotu

Badaƙalar $6bn: Tsohon Ministan Wutar Lantarki Ya Gamu da Babbar Matsala a Kotu

  • Tsohon ministan wutar lantarki, Olu Agunloye ya yi rashin nasara a ƙarar da ake tuhumarsa kan badaƙalar aikin wutar Mambilla
  • Hukumar EFCC ta gurfanar da Agunloye ne kan tuhume-tuhume bakwai da suka shafi yadda aka ɓatar da Dala biliyan 6 a aikin wutar
  • Sai dai tsohon ministan ya ƙalubalanci EFCC cewa ba ta da hurumin bincikarsa, amma alkalin kotun ya yi watsi da lamarin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Babbar kotun birnin tarayya Abuja mai zama a Apa ta yi watsi da buƙatar da tsohon ministan wutar lantarki da ƙarafa, Olu Agunloye, ya gabatar a gabanta.

Tsohon ministan ya ƙalubalanci hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC) cewa ba ta da hurumin da za ta bincike shi.

Kara karanta wannan

Emefiele: Tsohon gwamnan CBN ya fara girbar abin da ya shuka wajen canjin kuɗi

Tsohon ministan wutar lantarki, Olu Agunloye.
Tsohon ministan wutar lantarki, Agunloye ya gamu da cikas a shari'ar da ake masa Hoto: Olu Agunloye, EFCC Nigeria
Asali: Twitter

EFCC ta gurfanar da Olu Agunloye a gaban kotu ne kan tuhume-tuhume bakwai da suka shafi damfarar kwangilar aikin wutar lantarki na Mambilla wanda ya kai Dalar Amurka biliyan 6.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Agunloye ya nemi dakatar da shari'ar

Ranar 8 ga watan Fabrairu, 2024, tsohon ministan ta hannun lauyansa, Adeola Adedipe (SAN) ga shigar da ƙorafi gaban kotu yana kalubalantar binciken da EFCC ke masa.

A rahoton Channels tv, Agunloye ya kalubalanci cewa EFCC ba ta da hurumin bincikarsa har ta gurfanar da shi kuma ita kanta kotun ba ta da hurumin sauraron wannan ƙarar.

EFCC ta musanta ikirarin Agunloye

Da yake mayar da martani, lauyan ɓangaren masu shigar da kara, Abba Muhammed, ya kalubalanci tsohon ministan a ranar 22 ga Fabrairu, 2024.

Lauyan EFCC ya yi watsi da buƙatar Agunloye na a dakatar da shari'ar, inda ya ce ta saɓawa tanadin sashi na 115(2) na kundin dokokin kafa hujja a shari'a.

Kara karanta wannan

Kotun Ingila ta yanke wa ɗan Najeriya hukunci bisa laifin kashe matarsa

Da yake yanke hukunci a ranar Laraba, mai shari’a Jude Onwuegbuzie ya yi fatali da bukatar Agunloye saboda rashin cancanta.

Kotu ta yi watsi da buƙatar

Alkalin ya ce sashe na 6 da na 7 na dokar kafa EFCC a 2004, ya ba hukumar ikon bincike da kuma gurfanarwa gaban kuliya kan duk wasu laifukan tattalin arziki da na kudi.

"Tun da tuhume-tuhumen da ke kan wanda ake zargi laifukan tattalin arziki da na kudi ne, bukatar da wanda ake kara ya kawo ba ta cancanta ba kuma an yi watsi da ita," in ji alkalin.

Daga nan sai alkalin ya dage sauraron karar har zuwa ranar 30 ga Mayu, 2024 don ci gaba da shari'ar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

EFCC ta ƙara maka Emefiele a kotu

A wani rahoton kuma Kotu ta bayar da belin tsohon gwamnan CBN Godwin Emefiele kan N300m bayan gurfanar da shi kan sababbin tuhume-tuhume.

Hukumar EFCC ta sake maida Emefiele gaban kotu kan zargin kashe N18.96bn wajen buga N684.5m na sababbin takardun Naira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262