Rikicin Rivers: EFCC Ta Na Neman Gwamnan PDP Ruwa a Jallo? Gaskiya Ta Fito

Rikicin Rivers: EFCC Ta Na Neman Gwamnan PDP Ruwa a Jallo? Gaskiya Ta Fito

  • Rahotanni da ake yadawa a intanet na cewa EFCC na neman Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ruwa a jallo ba gaskiya bane
  • Mun yi bincike kan wani rahoto da aka wallafa a dandalin sada zumunta wanda ya nuna cewa EFCC ta yi sanarwar neman Fubara
  • A shekarar 2022 ne EFCC ta ayyana Fubara a matsayin wanda take nema ruwa a jallo lokacin yana ke rike da mukamin babban akanta janar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Port Harcourt, Rivers – A yayin da rikicin siyasar jihar Rivers ke tsamari, an samu rahotannin yadda ake kara samun takun saka tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Nyesom Wike.

Wutar rikicin ta kara ruruwa ne a ranar Litinin, 13 ga watan Mayu, lokacin da gwamnan ya bayyana shirinsa na kafa wani kwamiti da zai binciki gwamnatin Wike.

Kara karanta wannan

Rivers: Gwamnan PDP ya ɗauki zafi, ya sha alwashin bincikar Ministan Bola Tinubu

Rahoton EFCC na neman Gwamna Fubara ruwa a jallo, karya ne
Babu kamshin gaskiya a rahoton cewa EFCC na neman Gwamna Fubara ruwa a jallo. Hoto: @SimFubaraKSC, @officialEFCC
Asali: Twitter

Inda labarin neman Gwamna Fubara ya fito

Sa’o’i kadan bayan haka, wani mai amfani da kafar sadarwar zamani ta X, mai suna @possible1001, ya yi ikirarin cewa hukumar EFCC ta ayyana Fubara a matsayin wanda ta ke nema ruwa a jallo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya wallafa cewa:

"Da dumi-dumi:
"Hukumar EFCC ta bayyana cewa tana neman babban akanta na jihar Ribas, Fubara Siminayi da wasu mutane 58 ruwa a jallo bisa zargin karkatar da Naira biliyan 435..."

Wannan labar dai 'karya ce tsagoronta' domin wani cikakken bincike da Legit.ng ta yi ya nuna cewa labarin ya riga ya yi hannun riga da abin da ke faruwa yanzu a jihar.

Duba sanarwar a nan kasa:

EFCC ta neman Gwamna Fubara ruwa a jallo?

Duk da cewa mai amfani da shafin na X din bai bayyana inda ya nemo labarin ba, amma dai ya yi amfani da hoton da EFCC ke wallafawa idan tana neman mutum ruwa a jallo, kuma ya makala hoton gwamnan a jiki.

Kara karanta wannan

"Wannan ai sata ce," NLC ta magantu kan karin kudin wutar lantari a Kogi

Ko da muka shigar da hoton zuwa ga 'Google Image' domin tantance sahihancin sa, mun gano cewa an fara dora hoton a intanet ne tun a watan Satumbar 2018.

A lokacin, hukumar EFCC ta ayyana Fubara, daraktan kudi na gwamnatin jihar Ribas a lokacin da wasu mambobin majalisar jihar uku a matsayin wadanda take nema ruwa a jallo.

Kammalawa: EFCC ba ta neman Fubara a yau

A watan Mayun 2022, mun rahoto cewa EFCC ta kuma bazama neman Fubara, wanda shi ne Akanta janar na jihar a lokacin domin ta kama shi.

Wannan na nufin cewa, rahoton da @possible1001 ya wallafa na cewa EFCC na neman Fubara ba rahoto ne na yanzu ba, tsohon labari ne ya wallafa domin cimma wata manufa.

Bugu da kari, Fubara a yanzu shi ne gwamna mai ci a jihar Rivers, kuma ya na da kariya daga dukkanin wata tuhuma har sai wa'adin mulkinsa ya kare.

Kara karanta wannan

George-Kelly Alabo: Dalilin da ya sa na yi murabus daga kwamishinan ayyuka na jihar Rivers

Yadda aka yi yunkurin tsige gwamna Fubara

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani tsohon kakakin majalisar jihar Rivers, Edison Ehie ya ba da labarin yadda aka ba 'yan majalisa kudi domin su sa hannu a tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara.

Hon. Edison Ehie wanda ya bayyana cewa bai karbi tayin kudin ba shi da wasu 'yan tsirarun 'yan majalisar jihar, ya ce an kulla masa babban sharri daga baya a kan hakan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel