Kasar waje
Hukumomi a kasar Nijar sun zargi Najeriya da Bola Tinubu da neman kawo cikas a mulkin sojoji a kasar inda ta ce yana hada baki da wasu ƙasashen duniya.
Zakaran da Allah ya nufa da cara! Fafaroma Francis ya tsallake shiryayyen harin hallaka shi. Ya fadi kokarin da 'yan sandan Iraqi su ka yi a ziyarar da ya kai kasar.
Gwamnatin Najeriya za ta binciki yadda aka sayar da jiragen Najeriya na kamfanin Azman ba tare da sanin gwamnatin Najeriya ba. NCAA ta ce hakan ya saba doka.
Dan gwagwarmayar kafa kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo ya bukaci Bola Tinubu ya ja kunnen mataimakinsa, Kashim Shettima kan sukar Kemi Badenoch da ke Burtaniya.
Mai kudin duniya watau Elon Musk ya na da dukiyar ta kusa kai Dala biliyan 450. A zamanin nan, ba a taba samun labarin mutumin da ya tara Dala biliyan 400 ba.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bar Najeriya. Ya nufi Dubai domin kaddamar da wata cibiya adana mai. Kamfanin Najeriya ne ya mallaki cibiyar.
Mu na sa ran Nijar, Mali da Burkina Faso za su dawo cikin ECOWAS. Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ne ya faɗi haka. Ya ce ana amfani da dabarun diplomasiyya kan batun.
Rundunar 'yan sanda ta mikawa NAPTIP mutane 1o da aka boye a wani gida da niyyar safararsu zuwa kasar Libya. NAPTIP ta ce za a mika mutanen ga iyalansu.
Shugaban kasar Jamus, Frank-Walter Steinmeier a shirya muhimman abubuwa a kasar nan. Ya sauka a fadar shugaban kasa inda zai gana da Tinubu da shugaban ECOWAS.
Kasar waje
Samu kari