Bidiyon Yadda Jirgin Kasa Ya Bi Ta Kan Mai Barci, Kuma Ya Rayu Ya Ba da Mamaki

Bidiyon Yadda Jirgin Kasa Ya Bi Ta Kan Mai Barci, Kuma Ya Rayu Ya Ba da Mamaki

  • Wani lamari mai ban mamaki ya auku, inda jirgin kasa ya bi ta kan wani mutum, amma aka yi sa’a yar ayu
  • Wannan lamari dai ya auku ne a kasar Peru, inda aka ruwaito cewa, mutumin ya kwankwadi barasa ne kafin ya kwanta a layin dogo
  • Ba wannan ne karon farko da irin wannan hadari ke aukuwa da mutane a kasar Peru, hakan ya sha aukuwa sau da yawa

Kasar Peru – Wani mutum mai shekaru 28 mai suna Juan Carlos Tello ya tsallake rijiya da baya bayan da jirgin kasa ya buge shi yayin da yake barci a kan layin dogo a Lima, Peru, a ranar Asabar, 8 ga Maris.

Rahotannin da Legit Hausa ke samu sun nuna cewa, Tello yana cikin maye lokacin da lamarin ya faru, kamar yadda jaridar People ta bayyana.

Bidiyon da aka yada a kafafen yada labarai kamar BBC da Al Jazeera ya nuna wani mutum—da ake zaton Tello ne—yana kwance a kan layin dogo, kansa na dosane a kan layin, yayin da kafafunsa ke rataye daga wani bangare mai tsayi na layin.

Kara karanta wannan

Duniya ta zo karshe: Annabin karya ya sake bayyana a Najeriya, ya ce ya ga Allah da idonsa

Yadda jirgin sama ya bi kan wani mashayi
Yadda jirgi ya bi kan wani dan kasar Peru
Asali: Getty Images

'Yan dakiku bayan haka, yayin da haske mai karfi ya bayyana a bayan mutumin, a daidai lokacin ne ya fara daga kansa kafin daga bisani jirgin ya bayyana a jikinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayani daga jami’an tsaron kasa

Bayan jirgin ya ja shi na dan lokaci, mutumin ya yi kokarin tashi daga layin dogon, kamar yadda jaridar ta bayyana.

Wani jami'in tsaro na yankin mai suna Janar Javier Avalos ya bayyana cewa:

"Jirgin ya buge shi amma wata mu'ujiza da ta faru, bai kashe shi ba."

Avalos ya kara da cewa, jirgin yana kan hanyarsa ne ta zuwa tsaunukan Andes na Peru kuma ya tsaya nan take bayan ya buge Tello, wanda ya samu raunuka kanana a hannunsa na hagu.

Halin da jama’ar yankin suka shiga

Wannan lamari ya jawo hankalin jama'a kan muhimmancin kula da tsaro a layukan dogo, musamman ga masu tafiya ko zama kusa da layin dogo yayin da suke cikin maye.

Kara karanta wannan

Yadda wani matashi ya kashe 'Admin' saboda an cire shi a dandalin WhatsApp

Haka kuma, ya nuna bukatar karin matakan tsaro don hana irin wannan hadari faruwa nan gaba don kare rayuka.

A watan Mayun bara, wani hadari ya faru a wannan layin dogon, inda mutane hudu suka mutu kuma fiye da 30 suka jikkata bayan wata motar bas ta yi karo da jirgin kasan kaya a tsakiyar Peru.

Jirgi ya bi kan wani dan kasa Peru
Yadda jirgi ya bi ta kan wani dan kasar Peru
Asali: Getty Images

Wannan ya nuna cewa akwai bukatar daukar matakai masu tsauri don inganta tsaro a layin dogo na kasar.

Ya kamata mutane su kiyaye kansu

Bugu da kari, a watan Agusta na shekarar 2024, wani mutum ya rasa ransa bayan jirgin kasan kaya ya buge shi yayin da yake kokarin ketare layin dogo a wannan layin dogon.

Wannan ya kara nuna muhimmancin fadakar da jama'a game da hadarin da ke tattare da rashin kula da tsaro a wuraren layin dogo.

Wannan lamari na baya-bayan nan ka iya zama gargadi ga jama'a kan muhimmancin kula da tsaron rayukansu a layin dogo, musamman ga masu tu’ammali da kayan maye.

Haka kuma, ya zama kira ga hukumomi su kara inganta matakan tsaro don hana irin wannan hadari faruwa nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.