Jam'iyyar APC
'Yan majalisar dokokin jihar Katsina sun cimma matsaya kan tazarcen Gwamna Dikko Umaru Radda a zaben 2027. Sun amince ya yi wa'adi na biyu a mulki.
Rahotanni sun ce wasu matasa a garin Toro a jihar Bauchi sun fusata inda suke ihu ga Sanata Shehu Buba bisa abin da suka kira rashin tabuka komai.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar SDP a zaben 2023, Adewole Adebayo, ya bayyana cewa masu komawa jam'iyyar APC na saukakawa 'yan Najeriya.
Dan majalisar tarayya daga jihar Delta, Hon. Ngozi Okolie ya sauya sheka daga LP zuwa APC a jihar Delta, yana mai cewa jam'iyyar ba ta da shugabanci mai kyau.
Yayin da ake tururuwa zuwa jam'iyyar APC, Gwamnatin Tarayya ta ce sauya sheka zuwa APC ba zai hana gurfanar da gwamnonin da ake zargi da cin hanci ba.
Jigon jam'iyyar APC kuma tsohon ɗan takarar da ya nemi tikiti a zaɓen 2019, Chief Charles Udeogaranya ya ayyana shirinsa na sake neman takara a zaɓen 2027.
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya ce rikicin cikin PDP ya hana shi kwanciyar hankali, don haka ya yanke shawarar barin jam'iyyar gabanin zaben 2027.
Kungiyar fararen hula a Zamfara ta Arewa ta bukaci tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle ya sake tsayawa takara a 2027 saboda nasarorinsa wajen yaki da rashin tsaro.
Z a ji cewa tsohon Minista, Muktar Shagari ya ce Arewa za ta marawa Tinubu baya a 2027, yayin da APC ta bayyana shi dan takararta a babban zabe mai zuwa.
Jam'iyyar APC
Samu kari