'Ba Mu Yi': Matasa Sun Yi Wa Sanata 'Ihu' a Ta'aziyyar Rasuwar Limami a Bauchi
- Rahotanni ce wasu matasa a garin Toro a jihar Bauchi sun fusata, har aka ji su na yi wa Sanata Shehu Buba ihu
- Wasu sun danganta fushin da zargin cewa Sanatan ne ya hana wasu 'yan asalin garin shiga horon soja da kuma rashin ayyuka
- Sai dai wani na kusa da sanatan, Nurudden Yakubu Haske ya ce suna tare da dan majalisar duk inda ya ke amma bai san da labarin ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Toro, Bauchi - Fusatattun matasa a Toro, hedikwatar Karamar Hukumar Toro a Bauchi, sun yi wa sanatan yankinsu ihu.
An ce matasan sun fito kwansu da kwarkwata suna nuna fushin su ga Sanata Shehu Umar Buba da ke wakiltarsu.

Asali: Twitter
Ana zargin an yiwa Sanata ihu a Bauchi
Tribune ta ce matasan daga jam’iyyu daban-daban sun fito tituna suna ihu da cewa, “Ba mu yi”, “Mun gaji da kai”.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya daga Toro da ta shaida lamarin ta ce abin ya faru da misalin karfe 8:00 na dare ranar Juma’a.
Sanatan ya ziyarci garin ne don yin ta’aziyya bisa rasuwar limami a Toro, Imam Abdulkadir Abubakar.
Kodayake ba a fayyace dalilin hakan ba, wasu sun danganta hakan da zargin cewa Sanatan ne ya hana wasu shiga aikin soja.
Menene ake zargin silar yi wa Sanatan?
Ana zargin cewa wasu mutane 12 daga yankin da aka zaba don shiga aikin soja an fitar da su bisa umarnin Sanatan.
An rawaito cewa duk da ya shiga garin da dare, matasa sun taru a titin Mallallawa suna ihu kuma suka zagaye motarsa.
Don kwantar da lamarin, an ce Sanatan ya basu kudi, amma matasan suka ki karba suka ce ba kudi suke bukata ba.
Matasan sun ce suna so su gana da Sanatan kai tsaye don tattauna matsalolin yankin da yadda za a tallafa musu.
Ko da yake ya amince da hakan, suka ci gaba da ihun “ba mu yi” har sai da ya bar garin.

Asali: Facebook
Sanata Buba ya ba da gudunmawar N5m
Yayin da yake ta’aziyya, Sanata Buba ya bayar da N5m ga iyalan mamacin da wasu tallafi ga wasu dattawa da mata.
Sanata Buba ya kuma yi alkawarin gina katanga a filin idi da hakar rijiyar burtsatse don rage matsalar ruwa a yankin.
Wata majiya ta ce:
“Don gaskiya, da hujjojin da nake da su, Sanatan bai san komai game da fitar da matasan ba.
“Ka san Toro cibiyar siyasa ce a Karamar Hukumar Toro, duk abin da ya faru a nan zai shafi sauran yankuna”.
Ta kara da cewa matasan na fushi ne saboda Sanatan ya kasa kawo musu ci gaba tun lokacin da aka zabe shi.
Legit Hausa ta yi magana da yaron sanatan
Nurudden Yakubu Haske ya yi martani kan zargin da ake yi, ya ce bai san da labarin ihun ba.
Ya ce:
"To, yanzu haka muna tare a tawagar sanatan, tare muka je Toro amma ban ga inda aka yi masa ihu ba."
Haske ya ce yanzu haka suna hanyar shiga Jos saboda duk garuruwan tare suka je da shi kuma babu wani labari kan haka.
Zargin ta'addanci: MURIC ta kare Sanata Buba
A wani labarin, an ji kungiyar MURIC ta yi Allah wadai da zargin Sanata Shehu Buba da ake yi da ɗaukar nauyin ta'addanci.
Kungiyar ta kare hakkin Musulmai ta ce babu hujjoji kan zargin sanatan wanda ya kasance haziki da ke hidimtawa al'ummarsa.
Hakan ya biyo bayan zargin da gwamnatin jihar Bauchi ta yi wa sanatan da daukar nauyin dan ta'adda zuwa aikin hajji.
Asali: Legit.ng