Arewa
Tsohon hadimin mataimakin shugaban kasa, Dr. Hakeem Baba Ahmed ya ce ba zai sake karɓar wani muƙami a gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ba.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa wasu shanu 18 sun mutu bayan kiwo a gonar da aka zuba magani a kauyen Vwei da ke karamar hukumar Riyom a Plateau.
Mummunar gobara ta tashi a kasuwar wayoyi ta Ilorin. An ce wutar lantarki ce ta haddasa gobarar. An dakile wutar cikin lokaci amma rumfuna 10 sun kone.
Rahotanni daga jihar Benue sun tabbatar da cewa jami'an tsaro sun kashe Aungwa Sesugh, wanda aka fi sani da Tino Brown, a harin Zaki-Biam da ke jihar Benue.
Gwamnatin Borno ta ce tsananin zafin rana ne ya haddasa tashin gobara a dakin ajiye makamai na barikin sojojin Giwa, ba wai hari ba ne aka kawo daga waje.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya zargi Dele Momodu da mara wa Atiku Abubakar saboda kudi, tare da zargin cewa tsohon dan takarar ne ya jawo masu matsala.
ACF ta bayyana cewa Arewa za ta mara wa 'yan takarar da za su tsaya a zaben 2027 baya ne kawai idan suna da aniyar kare da inganta muradun yankin.
Kungiyar ISWAP ta dauki nauyin kai harin bam a Rann, jihar Borno, inda mutane 26 suka mutu ciki har da mata da yara; wasu sun yi konewar da ba a iya gane su.
Rikicin siyasa ya ɓarke tsakanin gwamnan jihar Neja, Bago da mataimakinsa Yakubu Garba, wanda aka ce ya fara kwashe kaya daga gidan gwamnati, da zummar barin aiki.
Arewa
Samu kari