Arewa
Ƴan sanda sun tabbatar da sun mayar da dukkanin motocin tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, da suka kwace gidajensa. Kotu ce ta umarci yin hakan.
Tsohon sanatan Bauchi ta Arewa, Adamu Bulkachuwa ya bayyana cewa mutane sun yi masa gurguwar fahimta kan maganarsa a zaman karshe na majalisar dattawa ta tara.
Dan majalisar jihar Bauchi, Honarabul Ado Wakili ya rigamu gidan gaskiya kwanaki kadan kafin wa'adinsa ya kare bayan ya sha kaye a zaben da aka gudanar a jihar.
Gwamnan juhar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗda, da sauran gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma sun gana da shugaban kasa kan batun tsaro da noma da sauransu.
Wani matashi ya rasa ransa yayin da ake zargin ya shiga cikin tiransifoma don satar wayoyin ciki, ma'aikatar wuta ta gargadi mutane kan aikata hakan anan gaba.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano sun samu nasarar cafke wani matashi mai suna Nafi'u Suleiman da ya yi garkuwa da kansa da karban kudin fansa a wurin kawunsa.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta yi nasarar cafke mutane bakin haure 12 daga kasar Mali da Niger a birnin Kano, yayin da aka kama wasu bata gari 33 a samame.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce har yanzu bai yanke shawarar sauya sabbin masarautun da tsohon gwamna Ganduje ya yi ba, inda ya ce duk jita-jita ce.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ƙara wa'adin shekarun ritayar ma'aikatan lafiya a jihar daga shekara 35 zuwa 40 suna aiki ko shekara 65 da haihuwa
Arewa
Samu kari