Arewa
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya naɗa Bukar Tijani a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar. Tijani ya taɓa riƙe muƙamin minista a baya.
Wani matashi dan darikar Kwankwasiya a Kano ya bayyana yadda yake ji da darikar tasu, ya ce ko shi kansa Kwankwaso me wannar tafiya bai isa ya hana su bin ta ba
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana yadda dattawan Kiristoci daga Kaduna ta Kudu suka tuge Barnabas Bala daga kujerarsa a wa'adin farko.
Tsohon hadimin gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, ya bayyana inda gwamnan ya shiga bayan an dai na jin ɗuriyarsa a jihar. Ya ce gwamnan yana birnin tarayya Abuja
Tsohon gwamnan Zamfara, Ahmed Sani Yerima ya ce amaryarsa da aka yi ta cece kuce kan ƙarancin shekarunta a shekarun baya ta kai matakin digiri na biyu a jami'a.
Bayan da shugaban NUC ya yi murabus, ya ce ba zai amince da zuwa jami'ar kudi ba, zai dawo BUK domin ci gaba da aikinsa da ya saba na koyarwa kamar yadda yake.
Akalla mutane fiye da 2,000 ke tsare a barikin Giwa da ke Maiduguri a jihar Borno, mafi yawa daga cikin wadanda ke tsaren sun ce ba su san me suka aikata ba.
Wasu ɓata-gari da ake zaton ɗaukar nauyinsu aka yi sun kai farmaki kan sakatariyar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a jihar Kogi, sun yi barna mai yawa.
Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar ya yi Allah wadai da aika-aikar da aka yi a kasar Sweden inda ya ya bukaci da a yi binciken gaggawa don daukar mataki a kan haka.
Arewa
Samu kari