Majalisar Wakilai Ta Dakatar Da Shirin Mika Yankin Adamawa Ga Kasar Kamaru

Majalisar Wakilai Ta Dakatar Da Shirin Mika Yankin Adamawa Ga Kasar Kamaru

  • Kwamitin kula da iyaka a majalisar wakilai ta Najeriya ta ki amincewa da mika yankin Sina ga kasar Kamaru
  • Yankin da ake tababa a kai na cikin karamar hukumar Michika da ke jihar Adamawa wanda ke iyaka da kasar Kamaru
  • Shugabar kwamitin, Beni Lar ta ce ba za su lamunci hakan ba yayin da ta ce za su kai ziyarar bincike yankin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Majalisar Wakilai a Najeriya ta ki amincewa da shirin mika wani yankin karamar hukumar Michika da ke Adamawa ga kasar Kamaru.

Kwamitin majalisar ta kasa da kasa da ke kula da iyaka ita ta bayyana haka a ranar Talata 12 ga watan Satumba a Abuja.

Majalisa ta hana shirin mika yankin Adamawa ga Kamaru
Majalisar Wakilai A Najeriya. Hoto: National Assembly.
Asali: Facebook

Meye majalisar ta ce kan mika yankin ga Kamaru?

Shugabar kwamitin, Beni Lar ita ta bayyana haka inda ta ce Sina a Najeriya ta ke ba Kamaru ba, Premium Times ta tattaro.

Kara karanta wannan

Tiriliyan 87 Na Bashin Najeriya, Tinubu Ya Gaza Tabuka Komai, An Bayyana Wadanda Ke Bin Kasar Bashi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lar ta ce yanka iyakar dole a dakatar da shi har sai an warware matsalar da ke tsakani.

Ta kara da cewa kwamitin zai ziyarci jihar Adamawa don kara samun bayanai kan iyakar da ake magana a kai.

Ta ce:

"Idan ba a mantaba mun yi irin wannan a jihar Kuros River wanda kakakin majalisar ya kara saka Sina a cikin ayyukan kwamitin.
"Kwamitin zai kai ziyarar bincike jihar Adamawa, mun riga sun sanar da gwamnan jihar kan wannan shiri namu."

Meye daraktan hukumar ya ce kan Kamaru?

Ta ce kwamitin ya gano cewa babu barikin sojoji da kuma tantuna na jami'an tsaro a iyakar Najeriya da Kamaru, cewar The Guardian.

Da ya ke magana, daraktan hukumar iyaka ta kasa, Adamu Adaji ya ce an yanka iyakar ne bisa dokar Kotun Kasa da Kasa (ICJ).

Kara karanta wannan

A Kokarin Gyara A Harkar Ilimi, Abba Kabir Ya Dauki Mummunan Mataki Kan Wasu Shugabannin Makarantu 2 A Kano

Wakilin yankin Sina, Adamu Kamale ya ce asali wannan yanki na Najeriya ne ba Kamaru ba inda ya ce ba a saka yankin a tsarin yanka iyaka ba.

Majalisa Ta Musanta Batun Ba Mambobinta Tallafin N100m

A wani labarin, Majalisar wakilai ta musanta batun da kungiyar kwadago ta Kasa (NLC), ta yi na cewa Gwamnatin Tarayya ta ba mambobinta N100m a matsayin tallafi.

Mataimakin sakataren Kungiyar NLC na kasa, Christopher Onyeka, shi ne ya yi zargin a wata sanarwa a birnin Tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel