Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa kan Duban Jinjirin Watan Musulunci

Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa kan Duban Jinjirin Watan Musulunci

  • Sarkin Musulmi ya buƙaci Musulmi a faɗin Najeriya su nemi jinjirin watan Jimada Saniya a ranar Litinin, 9 ga Nuwamba, 2026
  • Sanarwar fadar Sarkin Musulmi ta ce ranar ta yi daidai da 29 ga watan Jimada ƊUla na shekarar 1448 bayan hijira
  • An buƙaci duk wanda ya ga jinjirin watan ya kai rahoto ga shugaban ƙauye ko hakimi mafi kusa da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi magana game da sake duban wata a Najeriya.

Sarkin ya buƙaci Musulmi a faɗin Najeriya su fita neman jinjirin watan Jimada Saniya na shekarar 1448 bayan hijira a ranar Litinin, 9 ga Nuwamba, 2026.

Sarkin Musulmi ya magantu kan duba wata
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III. Hoto: The Sultanate Council Media Team.
Source: Facebook

Sanarwar Sarkin Musulmi kan duban wata

Hakan na cikin wata sanarwar da majalisar masarautar Sakkwato ta fitar, wadda Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya sanya wa hannu, cewar NTA News.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya ta faɗi yankuna da jihohin da su ci moriyar tallafin N50,000

Sanarwar ta buƙaci Musulmi su fita neman jinjirin watan, tare da kai rahoton duk wanda ya tabbatar da ganinsa ga shugaban ƙauye ko hakimi mafi kusa da shi.

Haka kuma, ta bayyana cewa ya kamata a isar da rahotannin ganin watan ta hannun hukumomin gargajiya zuwa ga Sarkin Musulmi domin ɗaukar matakin da ya dace.

An buƙaci Musulman da suka ga sabon jinjirin watan da su kai rahoton ganinsa ga shugaban gundumarsu ko dagacinsu mafi kusa domin isar da saƙon ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi.

Sanarwar ta ce:

“Saboda haka, ana buƙatar Musulmi da su fara neman jinjirin watan Jimada Saniya na shekarar 1448 bayan hijira a ranar Litinin, tare da kai rahoton ganinsa ga shugaban gunduma ko dagacinsu mafi kusa domin isar da saƙon ga Mai Alfarma, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar CFR, Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA).”

Sanarwar ta ƙara da cewa ya kamata a bi ta hannun hukumomin gargajiya wajen isar da rahotannin tabbataccen ganin jinjirin watan, domin bai wa Sarkin Musulmi damar ɗaukar matakin da ya dace.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda Lawal ya gayyaci Sarki Sanusi II bude masallaci a Zamfara

Haka kuma, majalisar ta yi kira ga Musulmi da su roƙi Allah Ya ba su shiriya da taimako wajen sauke wannan nauyin addini, kamar yadda rahoton Punch ya ce.

Sanarwar ta ƙara da cewa:

“Allah Maɗaukakin Sarki Ya taimake mu wajen sauke wannan nauyin addini. Amin.”

Sarkin Musulmi ya umarci duba wata a Najeriya

A baya, an ji cewa Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya buƙaci Musulmi su fara shirin duban jinjirin watan Jumada Ula na shekarar 1448.

Sultan ya buƙaci duk wanda ya ga jinjirin watan ya sanar da dagacin garinsu ko na ƙauye mafi kusa domin isar da sakon.

Sakamakon aikin duban watan zai tabbatar da ranar fara watan Jumadal Ula, yayin da watan Ramadan je kara gabatowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.