'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Fasto Da Wasu Mutum 2 A Jihar Plateau

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Fasto Da Wasu Mutum 2 A Jihar Plateau

  • Jimami yayin da 'yan bindiga su ka yi garkuwa da wani Fasto da kuma wasu mutane biyu a jihar Plateau
  • An kama Faston ne mai suna Usman Umaru a kauyen Maigemu da ke karamar hukumar Jos ta Gabas a cikin jihar Plateau
  • Wani daga cikin shugabannin matasa a yankin, Michael Madaki ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Plateau - Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da wani Fasto mai suna Usman Umaru a jihar Plateau.

Masu garkuwan sun dauke Faston ne a karamar hukumar Jos ta Gabas a jiya Laraba 13 ga watan Satumba.

Yan bindiga sun sace Fasto da wasu mutum biyu a jihar Plateau
'Yan Bindiga Sun Sace Wani Shahararren Fasto A Jihar Plateau. Hoto: The Guardian.
Asali: UGC

Yaushe aka sace Faston a jihar Plateau?

Punch ta tattaro cewa Faston wanda ke jagorantar Evangelical Church Winning All an kama shi tare da wasu mutane biyu a kauyen Maigemu.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Malamin Addini Da Wasu Mutum 3 a Wata Jihar Arewa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani shugaban matasa a yankin, Michael Madaki shi ya bayyana haka ga manema labarai a Jos, Ripples ta tattaro.

Madaki ya ce tun bayan garkuwa da malamin, an sanar da jami'an tsaro kuma sun bazama neman 'yan ta'addan a cikin daji.

Meye mutanen yankin ke cewa kan sace Faston?

Madaki ya ce:

"A ranar Laraba 13 ga watan Satumba, 'yan bindiga sun durfafi kauyen Maigemu tare da sace Fasto Usman Umaru.
"Har ila yau, sun kuma sace mutane biyu namiji mai suna Agwom Dauda da mace a cikin cocin.
"Tun bayan sace mutanen, jami'an tsaro da su ka hada da 'Operation Safe Haven' sun bazama daji neman 'yan bindigan."

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Alfred Alabo bai amsa kirar waya da aka yi masa ba don tabbatar da faruwar lamarin, Head Topics ta tattaro.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: 'Yan Bindiga Sun Farmaki Motocin Gwamnatin Jihar Arewa, Sun Sace Aƙalla Mutane 10

Yan Bindiga Sun Kai Hari A Plateau, Sun Hallaka Mutane 11

A wani labarin, A sabon hari da aka kai a kauyen Kulben da ke karamar hukumar Mangu na jihar Plateau ya hallaka mutane 11.

Harin wanda aka kai a daren jiya Lahadi 10 ga watan Satumba ya yi sanadiyar raunata mutane da dama da kuma asarar dukiyoyi.

Mafi yawancin wadanda abin ya shafa su ne ‘yan banga da su ke ran gadi don tsaron yankunan daga hare-haren ;yan bindiga a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel