Shugaban Jami'ar BUK Ya Bayyana Cewa Tsadar Rayuwa Ce Ta Saka Su Kara Kudin Makaranta

Shugaban Jami'ar BUK Ya Bayyana Cewa Tsadar Rayuwa Ce Ta Saka Su Kara Kudin Makaranta

  • Shugaban jami'ar Bayero da ke jihar Kano ya bayyana dalilin da yasa su ka kara kudin makaranta
  • Farfesa Sagir Abbas ya bayyana haka ne yayin hira da manema labarai a jiya Litinin 11 ga watan Satumba
  • Ya ce yanayin halin da ake ciki ya saka dole su ka kara kudin, idan ba haka ba sai dai a kulle makaranta

Jihar Kano - Shugaban jami'ar Ado Bayero (BUK), Farfesa Sagir Abbas ya bayyana dalilin da ya sa su ka kara kudin makaranta.

Farfesa Sagir ya bayyana haka a jiya Litinin 11 ga watan Satumba yayin hira da DW Hausa.

Dalilin kara kudin makaranta a BUK
Shugaban Jami'ar BUK Ya Yi Martani Kan Karin Kudin Makaranta. Hoto: Information Nigeria.
Asali: Facebook

Meye dalilin karin kudin a BUK?

Sagir ya ce dole ne ta saka hakan ganin yadda cire tallafin mai ya gurgunta al'amura tare da kara farashin kayayyaki a kasar.

Kara karanta wannan

A Kokarin Gyara A Harkar Ilimi, Abba Kabir Ya Dauki Mummunan Mataki Kan Wasu Shugabannin Makarantu 2 A Kano

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan na zuwa ne bayan manyan makarantu da dama a kasar sun kara kudin makaranta na dalibai.

Farfesa Sagir ya ce a baya kudin da dalibai ke biya bai wuce Naira dubu 27 ba wanda idan aka kwatanta da yanzu nawa ne kudin wanda ko Dala 100 ba ta kai ba.

Ya ce ganin yadda abubuwa su ka tashi musamman sufuri ya saka ma'aikatansu da yawa sun ajiye ababan hawansu a gida.

Ya ce:

"A baya dubu 27 yaro ke biya a makaranta idan ka duba nawa ne kudin ko Dala dari ba ta kai ba.
"Idan ka duba yanayin da ake ciki ko dai ayi karin kamar yadda mu ka yi ko a rufe makarantun ba za ayi karatun ba.
"Wannan shi ne yanayin da mu ka samu kan mu, komai ya ninka sau biyu ko uku, kamar yadda kaya a kasuwa su ka kara kudi, mu ma haka mu ke fita siyo kaya a kasuwa don gudanar da makaranta."

Kara karanta wannan

Tallafi: Yayin Da Ake Halin Kunci, Matasa Sun Yi Warwason Shinkafa Kan Motoci 3 A Arewa, Bayanai Sun Fito

Shugaban jami'ar BUK ya yabi Abba Gida Gida

Farfesan ya ce akwai ma'aikatansu da su ka ajiye ababan hawansu saboda yanayin rayuwa, sun samar musu motoci da ake jigilarsu zuwa da dawo wa.

Har ila yau, ya ce kananan ma'aikata ma an ba su lamunin kekuna da za su biya cikin watanni shida.

A karshe ya yabawa Gwamna Abba Kabir kan shirin da ya yi na biyawa dalibai 'yan asalin jihar Kano kudin makaranta.

Ya ce shi kansa ya nemawa dalibai taimako a wurin masu kudi, yanzu haka kaso 65 sun biya kudin makaranta.

Abba Kabir zai biya wa dalibai kudin makaranta a BUK

A wani labarin, Gwamnatin jihar Kano ta amince da sakin kudi Naira miliyan 700 domin biya wa dalibai 'yan asalin jihar a jami'ar Bayero kudin makaranta.

Gwamna Abba Kabir ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, 23 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel