'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari A Jihar Plateau, Sun Hallaka Mutane 11

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari A Jihar Plateau, Sun Hallaka Mutane 11

  • ‘Yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari a kauyen Kulben da ke karamar hukumar Mangu a jihar Plateau
  • Yankuna da dama a jihar musamman karamar hukumar Mangu ta sha fama da hare-haren ‘yan bindiga
  • Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Alfred Alabo ya tabbatar da faruwar harin inda ya ce su na jiran cikakken rahoto

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Plateau – A wani sabon hari da aka kai a kauyen Kulben da ke karamar hukumar Mangu na jihar Plateau ya hallaka mutane 11.

Harin wanda aka kai a daren jiya Lahadi 10 ga watan Satumba ya yi sanadiyar raunata mutane da dama da kuma asarar dukiyoyi.

'Yan bindiga sun hallaka mutane 11 a Plateau
Jihar Plateau na fama da hare-haren 'yan bindiga a yankuna da dama. Hoto: Caleb Mutfwang.
Asali: Twitter

Su waye 'yan bindigan su ka hallaka a Plateau?

Mafi yawancin wadanda abin ya shafa su ne ‘yan banga da su ke ran gadi don tsaron yankunan, Vanguard ta tattaro.

Kara karanta wannan

Tallafi: Yayin Da Ake Halin Kunci, Matasa Sun Yi Warwason Shinkafa Kan Motoci 3 A Arewa, Bayanai Sun Fito

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani matashi a yankin, Nanret Ishaya ya bayyana cewa Fulani ne su ka kai harin da misalin karfe 10 na dare.

Ya ce:

“Wasu Fulani dauke da makamai sun kawo hari kauyen Kulben da misalin karfe 10 na dare inda su ka yi ajalin mutane 11 da raunata da dama.
“A yanzu haka ana ta kokarin shirye-shiryen binne wadanda su ka mutu yayin da kuma aka yi asarar dukiyoyi da dama.

Sanatan da ke wakiltar Plateau ta Tsakiya, Diket Plang ya tabbatar da faruwar harin inda ya ce sun samu labarin cewa mutane 11 sun rasa ransu dalilin harin.

Kokarin jin ta bakin mai yada labarai na rundunar sojin ‘Operation Safe Haven’ Kyaftin James Oya ya ci tura yayin tattara wannan rahoto.

Meye 'yan sanda su ka ce kan harin a Plateau?

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Harbi ‘Dan Sanda, Sun Sace Mai Daki da Yarinyarsa Ya Na Kallo

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Alfred Alabo ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, cewar Leadership.

Ya ce:

“Mun samu labarin cewa wani abu ya faru a ranar Lahadi 10 ga watan Satumba da dare.
“Jami’in ‘yan sanda na yanki ya na kan aiki tun karfe 2 na dare, mu na jiran rahoton da zai kai zuwa hedikwatar ‘yan sanda.”

'Yan bindiga sun hallaka mutum 5 a kauyen Plateau

A wani labarin, Akalla mutum bakwai suka halaka bayan 'yan bindiga sun kai hari a kauyen Kerang cikin karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau.

Harin ya faru a kauyen ne duk da dokar ta baci ta sa'o'i 24 da gwamnatin jihar ta sanya a karamar hukumar biyo bayan hare-haren da 'yan bindiga suka kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.