Hankalin Netanyahu Ya Tashi ana Shirin Kafa Gwamnatin Isra'ila, Ya Yi Fade Fade

Hankalin Netanyahu Ya Tashi ana Shirin Kafa Gwamnatin Isra'ila, Ya Yi Fade Fade

  • Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi gargadin cewa haɗin gwiwar jam’iyyun adawa da Larabawa zai iya haddasa rugujewar ƙasar Isra’ila
  • Jagoran adawa, Gadi Eisenkot, na ƙoƙarin haɗa kai da wasu jam’iyyun Yahudawa da Larabawa domin kafa sabuwar gwamnati
  • Shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, ya nuna cewa Eisenkot na samun goyon bayan ’yan majalisa fiye da Netanyahu wajen kafa gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Israel - Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi gargaɗin cewa haɗin gwiwar jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin Larabawa wajen kafa sabuwar gwamnati zai iya haddasa rugujewar ƙasar Isra’ila.

Netanyahu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, yayin da ake jiran shugaban ƙasar, Isaac Herzog, ya sanar da wanda zai ba wa damar kafa sabuwar gwamnati bayan zaɓen ranar 27 ga Oktoba.

Netanyahu ya fara fade fade ana shirin kafa gwamnati
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu yana jawabi a Jerusalem. Hoto: Ronen Zvulun / POOL / AFP).
Source: Getty Images

Netanyahu ya fadi illar biye wa Larabawa

Kara karanta wannan

Shugaban Isra'ila ya zaɓi Eisenkot maimakon Netanyahu a kafa sabuwar gwamnati

Firaministan ya ce duk wata gwamnati da ta dogara da goyon bayan jam’iyyun masu akidar Musulunci za ta iya rusa Isra’ila daga cikin gida, cewar Al Jazeera.

Ya ce:

“Irin wannan gwamnati da ta dogara da masu kishin Musulunci za ta ruguza ƙasar Isra’ila daga cikin gida, kamar yadda yake faruwa a wasu ƙasashen Turai, har ma fiye da haka.”

Gargadin nasa na zuwa ne yayin da abokan hamayyarsa ke ƙoƙarin kawo ƙarshen mulkinsa, wanda ya kasance mafi tsawo a tarihin shugabannin Isra’ila.

Jagoran jam’iyyar adawa, Gadi Eisenkot, wanda tsohon babban hafsan sojin Isra’ila ne, ya buɗe ƙofar haɗin gwiwa da wasu jam’iyyun Yahudawa masu tsaurin ra’ayi da kuma ƙungiyoyin Larabawa.

Haɗin gwiwar na iya ba Eisenkot damar samun rinjayen da ake buƙata domin kafa gwamnati, tare da haɗin kan jam’iyyar Raam mai matsakaicin akidar Musulunci da kuma goyon bayan ƙungiyar Joint List mai rinjayen Larabawa.

A zaɓen da aka gudanar ranar 27 ga Oktoba, babu wani ɓangare da ya samu rinjayen kujerun da ake buƙata domin kafa gwamnati.

Shugaba Isaac Herzog ya bayyana cewa yana ganin Eisenkot ya cancanci samun damar kafa gwamnati, saboda ƙungiyoyin da suka mara masa baya suna da wakilai 67, sabanin 46 da suka nuna goyon baya ga ɓangaren Netanyahu.

Kara karanta wannan

Abin da ƴan Kwankwasiyya suka ce da kotu ta rushe takarar su Atiku

Sai dai Herzog ya kuma nuna sha’awarsa ga yiwuwar kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa da za ta ƙunshi ɓangarorin Yahudawa daga sansanoni daban-daban.

A nasa ɓangaren, Netanyahu ya sake nuna goyon bayansa ga kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa, wadda za ta haɗa dukkan jam’iyyun da ke goyon bayan ra’ayin kishin ƙasar Isra’ila.

Sai dai jam’iyyar Yashar ta Eisenkot ta mayar da martani, inda ta buƙaci jam’iyyar Likud ta Netanyahu da abokan haɗin gwiwarta su raba gari da jam’iyyun masu tsaurin ra’ayi, sannan su shiga gwamnatin da Eisenkot zai jagoranta.

Jam'iyyu sun kwaye wa Netanyahu zabi

An ji cewa babbar kungiyar jam’iyyun Larabawa a Isra’ila ta sanar da goyon bayanta ga Gadi Eisenkot domin ya kafa sabuwar gwamnati.

Jam’iyyar United Torah Judaism ta ki marawa Benjamin Netanyahu baya, lamarin da ya kara raunana matsayinsa.

Jam’iyyun sun samu kujeru 19 a zaben da aka gudanar, abin da ya kara musu muhimmanci wajen tantance wanda zai jagoranci Isra’ila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.