Abu Ya Gagara Karewa: Gwamna Radda Ya Fadi Yadda Zai Dakile Matsalar Tsaro

Abu Ya Gagara Karewa: Gwamna Radda Ya Fadi Yadda Zai Dakile Matsalar Tsaro

  • Gwamnan Katsina, Dikko Radda, ya sha alwashin ƙarfafa yaƙi da rashin tsaro a ƙaramar hukumar Matazu ta jihar
  • Hakimin Matazu ya bayyana cewa yankin bai fuskanci wani harin tsaro ba cikin kwanaki 45 da suka gabata
  • Ɗan majalisar Musawa/Matazu ya ce an raba babura sama da 2,000 da tallafin N50,000 ga mata da ɗalibai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Matazu, Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya sake tabbatar da aniyarsa ta kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a ƙaramar hukumar Matazu ta jihar.

Radda ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ƙarfafa haɗin gwiwa da jami'an tsaro, sarakunan gargajiya da shugabannin al'umma domin kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

Radda ya dauki alkawari kan matsalar tsaro
Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina. Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda.
Source: Facebook

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin ziyarar da ya kai ga Hakimin Matazu, Alhaji Iro Maikano, gabanin gangamin kamfen ɗin Tinubu-Dikko na zaɓen 2027, cewar Arise News.

Kara karanta wannan

"Nan ba da daɗewa ba yan Najeriya za su fara murna da tsare tsaren Shugaba Tinubu"

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tare da jami'an tsaro da shugabannin al'umma domin ƙarfafa nasarorin da aka samu wajen yaƙi da rashin tsaro.

Radda ya kuma yaba wa al'ummar Matazu bisa goyon baya da haɗin kai da suke bai wa gwamnatinsa, musamman a zaɓukan da suka gabata.

An shafe kwanaki 45 ba tare da harin tsaro ba

Da yake nasa jawabin, Hakimin Matazu, Alhaji Iro Maikano, ya bayyana cewa yankin bai fuskanci wani harin tsaro ba cikin kwanaki 45 da suka gabata.

Ya danganta hakan da haɗin gwiwar jami'an tsaro, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki a yankin.

Hakimin ya yaba wa gwamnatin Radda bisa haɗa ayyukan tsaro da tattaunawa tsakanin manoma, makiyaya da shugabannin al'umma domin samar da zaman lafiya.

Ya kuma nuna godiya kan ayyukan titin Sarki Duku da hanyar da ta haɗa Giyanka da hanyar Sarki Duku, yana mai cewa sun inganta sufuri da zirga-zirga.

Kara karanta wannan

Matasa sun hargitsa wajen da Shettima ya je kamfe din APC na 2027

Gwamna ya gano hanyar magance matsalar tsaro a Katsina
Taswirar jihar Katsina da ke fama da hare-haren yan bindiga. Hoto: Legit.
Source: Original

APC ta fara shirin zaɓen 2027

A nasa jawabin, shugaban APC na jihar Katsina, Bishir Gambo, ya buƙaci mazauna Matazu su ci gaba da goyon bayan jam'iyyar a zaɓen 2027.

Ya tuna cewa jam'iyyar adawa ba ta samu gagarumin goyon baya a yankin ba a zaɓen 2023, inda ya buƙaci mazauna yankin su maimaita hakan a zaɓe mai zuwa.

Shi ma ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Musawa/Matazu, Abdullahi Aliyu Ahmed, ya yi ikirarin cewa kusan kashi 99 cikin 100 na al'ummar Matazu na goyon bayan APC.

Ya bayyana cewa shirye-shiryen tallafa wa jama'a a yankin sun haɗa da rabon babura sama da 2,000, tallafin N50,000 ga mata da kuma tallafin karatu na N50,000 ga ɗalibai

Radda ya magantu kan kamfen dinsa

A wani labarin, an ji cewa Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya bayyana abin da zai yi yakin neman zabe da shi a kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Yadda Iran ta 'jawo wa' Trump faduwa zabe a Amurka, ya ce ya yi mamaki

Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa ba zai yi wa jama'a sababbin alkawura ba domin neman su sake ba shi kuri'unsu a zaben 2027.

Gwamnan ya bayyana cewa zai nuna ayyukan da ya gudanar domin su zama abubuwan da zai yi yakin neman zabe da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.