Kashim Shettima Zai Yi Rabon Kayan Abinci a Jihohin Arewa Maso Gabas Don Ragewa Al’umma Radadi

Kashim Shettima Zai Yi Rabon Kayan Abinci a Jihohin Arewa Maso Gabas Don Ragewa Al’umma Radadi

  • Mataimakin shugaban kasan Najeriya, Kashim Shettima ya kaddamar da rabon abinci a Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Gwamnonin jihohin Arewa maso Gabas sun yi taronsu na wata-wata a jihar Borno, wannan ne karon farko da haka ta faru
  • Za a yi katafaren aikin titi daga wani yankin Borno zuwa yankin don saukaka zirga-zirga da hade al’ummomi

Maiduguri, jihar Borno - Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya yi kira ga hukumar raya shiyyar Arewa maso Gabas (NEDC) da ta fadada ayyukan da take yi a shiyyar domin kara yawan ayyukan tituna.

Sanata Shettima ya yi wannan kiran ne a ranar Asabar yayin da yake kaddamar da rabon kayan abinci na Naira biliyan 15 ga gwamnonin yankin da kuma gina titi mai tsawon kilomita 22 a hanyar Mafa a Maiduguri ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Nasarorin da Gwamnati 7 Ta Samu Cikin ‘Yan Kwanakin da Bola Tinubu Ya yi a Indiya

Taron na hukumar NEDC ya yi ya zo daidai da taron kungiyar gwamnonin yankin Arewa maso Gabas, wanda aka gudanar a karon farko a 2023 a gidan gwamnati da ke Maiduguri.

Shettima ya kaddamar da shirin rabon abinci
Za a yi rabon abinci a jihohin Arewa maso Gabas | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A taron akwai mai masaukin baki gwamnan jihar Farfesa Babagana Zulum da daukacin gwamnonin yankin na Arewa maso Yamma, Channels Tv ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An kaddamar da aikin titi a jihar Borno

Mataimakin shugaban kasar ya kaddamar da aikin gina titi mai nisan kilomita 22.5 wanda zai hada al'ummomi da dama a karamar hukumar Jere da wasu sassa na karamar hukumar Mafa.

Shettima ya jagoranci wasu manyan baki zuwa babban dakin taro na fadar gwamnatin jihar, inda gwamnonin Arewa maso Gabas suke gudanar da taronsu na wata-wata.

Manajin Daraktan NEDC, Mista Mohammed Goni Alkali ne ya gabatar da jawabin maraba, wanda daga bisani Shettima ya yi karin haske.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Zabe: Shettima Ya Sake Shan Caccaka Kan Batun Yi Wa Atiku Ritaya

Bayan haka mataimakin shugaban kasan ya bar Maiduguri zuwa Abuja inda daga nan ne zai kai ziyara jihar Kebbi domin kaddamar da gina gidaje 1,000 a fadin jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Za a yi rabon abinci a Zamfara

A wani labarin, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, a ranar Talata ya kaddamar da rabon kayan tallafi a jihar.

Gwamnan ya nanata cewa rabon kayan tallafin abincin na dukkanin al'ummar jihar ne ba tare da la'akari daga jam'iyyun da suka fito ba.

A wajen kaddamar da rabon kayan tallafin, Dauda ya yi kira ga kwamitin da aka dora alhakin rabon kayan a kansu, da su tabbatar sun yi gaskiya da adalci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.