Okowa: Abokin Takarar Atiku a 2023 Ya Bayyana Dalilin da Yasa Suka Raba Gari Ya Koma APC
- Ifeanyi Okowa, tsohon abokin takarar Atiku a zaɓen 2023, ya ce ya sauya sheƙa zuwa APC saboda ya gamsu da ayyukan Shugaba Bola Tinubu
- Okowa ya bayyana cewa gyare-gyaren tattalin arziƙin gwamnatin Tinubu sun ƙara kuɗaɗen da jihohi da ƙananan hukumomi ke samu
- Tsohon gwamnan ya taɓa bayyana nadamarsa kan amincewa da zama mataimakin Atiku a zaɓen shugaban ƙasa na 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Rivers - Tsohon gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, wanda shi ne ɗan takarar sanatan Delta ta Arewa a ƙarƙashin jam'iyyar APC, ya yi magana kan janye goyon bayansa ga Atiku Abubakar.
Ifeanyi Okowa ya ce ya janye goyon bayansa ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, domin ya fahimci abin da Shugaba Bola Tinubu ke yi wa Najeriya.

Source: Facebook
The Cable ta ce Okowa, wanda ya kasance abokin takarar Atiku a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, ya bayyana hakan ne ranar Asabar, 7 ga watan Nuwamban 2026 yayin taron yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Fatakwal, babban birnin Jihar Rivers.

Kara karanta wannan
2027: Shugaban majalisa ya bayyana abin da ya zama dole ga 'yan Najeriya kan Tinubu
Ya ce ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC ne saboda ya yi imanin cewa gwamnatin Tinubu tana ɗaukar matakai masu wahala, amma wajibi ne domin magance matsalolin tattalin arziƙin Najeriya da suka daɗe.
Okowa ya ce ya fahimci manufofin Tinubu
Tsohon gwamnan ya tuna cewa a zaɓen 2023 yana tare da Atiku a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, amma yanzu ya gamsu da salon mulkin shugaban ƙasar.
A kalamansa:
“Kowa ya san cewa a shekarar 2023 ina cikin wata tawaga ta daban, amma yanzu na ga haske, kuma na fahimci abin da shugaban ƙasa yake yi wa Najeriya.
"Abin da ake yi shi ne daidai, kuma tun da daɗewa na koma APC domin haɗa kai da shugaban ƙasa, saboda da gaske yana gina sabuwar Najeriya.”
Okowa ya ce Tinubu ya fahimci cewa gwamnatocin da suka gabata sun lalata tubalan da ake buƙata wajen gina tattalin arziƙin ƙasa, don haka yana ƙoƙarin gyara su.
Ya bayyana cewa Najeriya tana kan hanya mai kyau saboda ana sake gina ginshiƙan tattalin arziƙin ƙasar.
Ya yaba da rabon kuɗaɗen tarayya
Okowa ya ce gyare-gyaren kuɗaɗen shiga da gwamnatin tarayya ta yi sun taimaka wajen ƙara yawan kuɗaɗen da ake rabawa jihohi da ƙananan hukumomi.
A cewarsa, hakan ya ba gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi damar gudanar da ayyukan raya ƙasa, biyan albashi da kuma biyan haƙƙoƙin ma'aikatan gwamnati da 'yan fansho.
"A yau, jihohinmu da ƙananan hukumominmu suna gudanar da ayyuka yadda ya kamata saboda shugaban ƙasa yana ci gaba da tattara kuɗaɗe domin rabawa jihohi da ƙananan hukumomi.
“Ba mu ƙara jin labarin mutane suna bin albashi ko kuɗin fansho ba. Ƙananan hukumomi suna gudanar da ayyuka, jihohi suna gudanar da ayyuka, kuma muna iya biyan albashi.” In ji shi.
Okowa ya ce irin nasarorin da aka samu a Legas a baya ana ƙoƙarin maimaita su a faɗin Najeriya.
Yadda Okowa ya zama abokin takarar Atiku
A shekarar 2022, Atiku Abubakar ya zaɓi Okowa a matsayin mataimakinsa domin fafatawa a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Wannan zaɓi ya haifar da saɓani a cikin PDP, domin wasu jiga-jigan jam'iyyar sun fi son Nyesom Wike, wanda a lokacin yake gwamnan Jihar Rivers, ya zama abokin takarar Atiku.
Daga ƙarshe, Atiku da Okowa sun fafata a zaɓen tare, amma suka sha kaye a hannun Tinubu na APC.
A watan Afrilun 2025, Okowa ya bayyana cewa yana nadamar amincewa da zama mataimakin Atiku a zaɓen.
Ya ce yankin Kudu na Najeriya yana son samar da wanda zai gaji tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, amma shugabannin PDP sun yanke shawarar da ta sa hakan bai samu ba.

Source: Facebook
Matsayar INEC kan takarar Atiku
A wani labarin kuma, kun ji cewa INEC ta ce ba za ta ɗauki matsaya kan rikicin shugabancin jam'iyyar ADC ba, har sai ta samu tare da nazarin sahihin kwafin hukuncin kotu.
Matakin na INEC ya biyo bayan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamban 2026 inda ta soke shugabancin kwamitin riƙon ƙwarya da David Mark ke jagoranta.
Asali: Legit.ng

