Fitaccen Mawaki Rarara Zai Gina Tituna Guda 7 a Wasu Yankunan Jihar Katsina

Fitaccen Mawaki Rarara Zai Gina Tituna Guda 7 a Wasu Yankunan Jihar Katsina

  • Fitaccen mawaki Rarara ya bayyana ba da ayyukan gina tituna a yankuna daban-daban na jihar Katsina a Arewa maso Yamma
  • An ruwaito cewa, za a yi titunan ne guda bakwai a wasu yankunan da aka bayyana a kananan hukumomin jihar
  • Jama’a sun yi martani, sun yi addu’ar Allah ya saka ga Rarara da kuma yi masa fatan alheri a rayuwarsa da aikinsa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Katsina - Dauda Adamu Abdullahi, wanda aka fi sani da Kahutu Rarara ya ba da aikin gina tituna guda bakwai a wasu yankunan jihar Katsina.

Wannan na fitowa ne daga bakin mai magana da yawunsa Rabi’u Gabra Gaya a lokacin da ya yada wasu hotunan aikin titi a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 10 Satumba, 2023.

A hotunan, an ga motocin kankare da ke sharbar kasa a kokarin yin aikin titi wani yankin da Gaya yace ana aikin ne a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

An kuma: Sanatan APC ya yi nasara kan PDP a gaban kotu, an yi watsi da duk wani zargi

Rarara ya ba da aikin gina tituna a Katsina
Yadda Rarara ya ba da aikin yin tituna a Katsina | Hoto: Rabi'u Garba Gaya
Asali: Facebook

Yadda titunan za su kasance a Katsina

Da yake yada hotunan, ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mai girma shugaban kasar wawaka Alhaji Dauda Kahutu Rarara, ya bada aikin titin Tudun Wakili zuwa Sundu zuwa Danja zuwa Garin Dabai, aikin titin zai wuce zuwa garin Kahutu daga Kahutu zai wuce zuwa garin Chediya, daga garin Chediya kwaltar zata wuce har Zarewa.
“Jama'ar wannan yankin suna godiya tare da fatan Allah ya raba ka da Hajiya lafiya.”

Martanin jama’a a kafar Facebook

Yunusa Haruna Dabai yace:

“Nima Nan shaidane, naga an fara daga sundu zuwa tudun wakili, Amma saidai yadda ka lissafo hanyoyi, akwai cakude acikin Bayanin naka ka sake bincike dai, Allah ya saka mashi da alheri Dauda Adamu Abdullahi.”

Abdoull Maina Abba yace:

“Rarara Gomnati Che da kanta.”

Khadeejat Ismail tace:

“Ubangiji yasaka masa da ma fificin alkairi.”

Kara karanta wannan

Cire tallafi: Shettima Zai rabawa talakawan jihohin Arewa 6 kayayyakin abinci

Sadisu Auwal Mai Lima yace:

“Ina kanon laifi taimai.”

Rabiu Musa Buhari Aqida yace:

“Allah yasaka masa da gidan Aljannah.”

Wike ya dauko aiki gadan-gadan

A wani labarin, hukumar FCTA mai kula da birnin tarayya ta bada umarnin ruguza wani tagwayen gini da aka kammala a birnin tarayya da ke Abuja.

A rahoton da aka samu daga Punch, an samu labari an yi wannan gini ne a wani fili da hukuma ba ta bada izini ba, saboda haka aka rusa ginin.

Ginin ya na kan fuloti mai lamba 226 Cad Zone A02 Wuse 1 a unguwar Zone 6 da ke birnin tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel