Arewa
Wasu mata da ke yin gurasa a Kano, sun yi zanga-zanga don nuna rashin jin dadinsu kan karin kudin fulawa, sun ce karin kudin ya jefa sana'arsu cikin wani hali.
Tsohon Akanta Janar a Najeriya, Ahmed Idris ya bayyana yadda hukumar EFCC ta yaudare shi kan amincewa da hannunsa a badakalar naira biliyan 109.4.
Masarautar Pindiga da ke ƙaramar Akko a jihar Gombe ta yi fatali da bukatar Sanata Danjuma Goje kan rushe masallatai 2 da ke masarautar don gyara su.
Kasa da kwanaki biyu da barin kujerar gwamnan Kogi, hotunan Yahaya Bello sun mamaye Abuja, inda ake tallata shi a matsayin mai neman kujerar shugaban jam'iyyar APC.
Sanata Kawu Sumaila ya ki amincewa da bukatar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na maye gurbin Babban daraktan dake kula da bangaren gas, Mansur Kuliya da Oluwole.
Gwamnatin jihar Kogi ta yi martani kan jita-jitar cewa ta kirkiri sabon ofishin tsohon gwamna, Yahaya Bello a cikin gidan gwamnati bayan Bello mika mulki
Wani abin tashin hankali ya faru a wani wurin da ake hakar ma'adanai a jihar Bauchi, inda mata hudu suka mutu nan take bayan da kasa ta rufta kan su.
Hukumar zaben jihar Nasarawa, NASIEC ta dage zaben da aka shirya gudanarwa a ranar 31 ga watan Agusta saboda shari'ar da ake yi da hukumar da wasu mutane 12.
Gwamna Babagana Umara Zulum ya amince da nadin Mutawali Shettima Bukar a matsayin sabon Wazirin Borno. Shehun Borno, Abubakar Elakanrmi ya mika sunan Bukar.
Arewa
Samu kari