APC: Fastocin Yahaya Bello Na Neman Kujerar Ganduje Sun Mamaye Abuja

APC: Fastocin Yahaya Bello Na Neman Kujerar Ganduje Sun Mamaye Abuja

  • A ranar Litinin ne aka tashi da wasu hotunan Yahaya Bello wanda ke nuna yana neman kujerar shugaban jam'iyyar APC na kasa
  • Yahaya Bello dai shi ne tsohon gwamnan jihar Kogi, kuma ko awanni 48 ba ayi da saukarsa ba aka ga sabbin fastocin sa a Abuja
  • Wata majiya daga jam'iyyar ta bayyana cewa ana wata makarkashiya don tsige Ganduje daga kujerar shugaban jam'iyyar don dora Bello

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Kasa da kwanaki biyu da barin kujerar gwamnan jihar Kogi, hotunan Yahaya Bello sun mamaye Abuja a ranar Litinin, inda ake tallata shi a matsayin mai neman kujerar shugaban jam'iyyar APC.

Abdullahi Umar Ganduje shine shugaban jam'iyyar na kasa a halin yanzu, wanda hakan ke nufin Yahaya Bello zai kara da shi wajen samun kujerar.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Jam'iyyar APC ta yi magana kan tsohon gwamnan arewa da ke son tsige Ganduje

APC: Fastocin Yahaya Bello na neman kujerar Ganduje sun mamaye Abuja.
APC: Fastocin Yahaya Bello na neman kujerar Ganduje sun mamaye Abuja. Hoto: @Miniko_jnr
Asali: Twitter

An zabi Ganduje ne a taron kwamitin zartarwa na jam'iyyar na kasa a ranar 3 ga Agusta, 2023, don maye gurbin Abdullahi Adamu wanda ya yi murabus daga mukamin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ga fastocin Yahaya Bello a Abuja

An ga fastocin tsohon gwamnan a manyan titunan birnin tarayya Abuja, musamman a kusa da sakatariyar gwamnatin tarayya, Tribune Online ta ruwaito.

An kuma ga fastocin a bango da shingen gine-ginen da ke kewaye da sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa da ke kan titin Blantyre, Wuse 2, Abuja.

Ana shirin karbe shugabancin APC daga hannun Ganduje

Fastocin tsohon gwamnan jihar Kogi an kawata su da rubutu kamar haka “Mataki na gaba a APC. Alhaji Yahaya Bello a matsayin shugaban jam'iyyar APC na kasa. Jagoran canji, gina kakkarfar APC.”

Majiyoyi a cikin jam’iyyar sun ce an kitsa yunkurin tsige Ganduje ne a ciki da wajen jam’iyyar, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Labari Mai Dadi: Shugaban jam'iyyar PDP a jihar Legas ya shaki iskar 'yanci

An kuma tattaro cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar daga shiyyar Arewa ta tsakiya ne ke son dawo da ofishin shugaban jam’iyyar na kasa hannun su wanda ke hannun Arewa maso Yamma inda Ganduje ya fito.

Duba fastocin a kasa kamar yadda @Miniko_jnr ya wallafa a shafinsa na Twitter:

Borno: Zulum ya kawo tsarin rijistar aiki ga ciyamomi

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya kawo sabon tsarin kiran rijistar halartar aiki ga ciyamomin kananan hukumomin jiharsa.

Zulum ya ce zai yi amfani da wata na'ura da ciyamomin za su rinka amsa rijistar sau hudu a rana don magance wadanda ke fashin zuwa aiki

Asali: Legit.ng

Online view pixel