'Yan Sanda Sun Kama Wasu Gungun Mutanen da Ake Zargi da Sace Akwatunan Zabe a Kano

'Yan Sanda Sun Kama Wasu Gungun Mutanen da Ake Zargi da Sace Akwatunan Zabe a Kano

  • Wasu tsagerun 'yan daba sun shiga hannun a daidai lokacin da ake kada kur'iu a jihar Kano ranar Asabar
  • An ruwaito cewa, an kame tsagerun dauke da muggan makamai, kuma ana zargin 'yan siyasa ne suka yi hayarsu
  • An bayyana dage ci gaba da kada kuri'u a wasu kananan hukumomin jihar Kano saboda rikicin da ya barke

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Jihar Kano - 'Yan sanda a jihar Kano sun yi nasarar kame wasu gungun mutanen da ake zargin sun sace akwatunan zabe a zaben maye gurbin da aka gudanar na 'yan majalisu.

Matasan da aka kamen an ce suna dauke da muggan makamai, kuma sun nufi tada hankali a zaben da aka yi a karamar hukumar Kunchi ta jihar.

Kara karanta wannan

Bayan shafe kusan mako a hannun 'yan bindiga, dalibai da malaman makaranta sun shaki iskar 'yanci

An tattaro cewa, wasu tsagerun matasa 'yan daba sun sace akwatunan zabe a karamar hukumar Tsanyawa duk dai a Kanon.

'Yan sanda sun kama 'yan daba a Kano
Yadda aka kame 'yan daba a Kano | Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai inda aka yi zabe lafiya?

Sai dai, abin farin ciki an ruwaito cewa, an yi zabe cikin kwanciyar hankali a karamar hukumar Kura, rahoton The Nation.

Jami'an tsaro sun hallara a runfunan zabe a Kura, inda hakan ya ba da gudunmawa ainun wajen wanzar da zaman lafiya.

Hakazalika, an ruwaito jama'a da dama sun fito sun kada kuri'unsu a inda aka yi zabe cikin kwanciyar hankali.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mohammed Usaini Gumel ya zanta da manema labarai kan kamen da aka yi.

Su wa suka yi hayar 'yan daban?

Ya ce, an kama matasan da muggan makamai, kuma ana zargin wasu gurbatattun 'yan siyasa ne suka yi hayarsu don dagula zaman lafiya a runfunan zaben.

Kara karanta wannan

Zaben cike gurbi: Masu zabe sun kulle jami'an INEC kan wani dalili a Jos, bayanai sun fito

Biyo bayan rikicin da ya auku, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanar da dage ci gaba da kada kuri'u a kananan hukumomin Tsanyawa da Kunchi a jihar ta Kano, Daily Post ta ruwaito.

A cewar kwamishinan yada labarai na INEC, dage ci gaba da zaben ya yi daidai da tanadin sashe na 24(3) a kudin zaben 2022.

Ya zuwa yanzu, hukumar ta ba al'umma hakuri, ta kuma ce tana ci gaba da bincike, wanda zuwa Litinin za ta zauna kan lamarin.

An sanar da sakamakon zabe a Kano

A wani labarin na daban, hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta sanar da sakamakon zaben cike gurbi a jihar Kano.

INEC ta fitar da sanarwar ce kan sakamakon zaben cike gurbi a mazabar Rimin Gado/Tofa a Majalisar jihar Kano.

Hukumar ta ayyana Bello Muhammad Butu-Butu na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Rimin Gado/Tofa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel