Aikin Gama Ya Gama: Dan Takarar PDP Ya Sha Kaye a Zaben Cike Gurbi a Yobe, an Fadi Wanda Ya Lashe

Aikin Gama Ya Gama: Dan Takarar PDP Ya Sha Kaye a Zaben Cike Gurbi a Yobe, an Fadi Wanda Ya Lashe

  • Rahoto ya bayyana yadda aka kayar da dan takarar sanata a jam’iyyar PDP a zaben da aka gudanar na cike gurbi a Yobe
  • Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka dakatar da zaben a wasu yankunan jihar Kano saboda barkewar rikici
  • A gefe guda, an alanta dan jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar jiya Asabar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Yobe - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Musa Mustapha a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na Sanatan Yobe ta Gabas da aka gudanar a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

'Za a gwabza': Mai tsare ragar tawagar Afrika ta Kudu ta shirya karawa da Super Eagles a gasar AFCON

Baturen zabe na INEC Farfesa Ibrahim Ahmed Jajere ne ya bayyana hakan a Damaturu, inda yace Sunda Mustapha ya samu kuri’u 68,778 tare da lallasa Aji Kolomi na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 18,878.

APC ta lashe zaben cike gurbi a Yobe
An bayyana wanda ya lashe zaben cike gurbi a Yobe | Hoto: @TopeBrown
Asali: Twitter

Punch ta ruwaito Farfesa Jajere yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Hon. Musa Mustapha na jam’iyyar APC, da ya samu mafi yawan kuri’un da aka kada, kuma ya cika sharuddan doka, an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi a Yobe ta Gabas”.

Ya zabe ya kasance a jihar Kano?

A wani rahoton da muka kawo a baya, an bayyana yadda 'yan sanda suka kame wasu bayan barna a jihar Kano.

Ya zuwa yanzu, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta dakatar da zaben a kananan hukumomin Tsanyawa da Kunchi a jihar.

Wannan na zuwa ne bayan da wasu tsageru da ake zargin 'yan siyasa ne suka yi hayarsu don tayar da hankalin jama'a.

Kara karanta wannan

INEC ta sanar da ɗan tsohon sifetan 'yan sanda wanda ya lashe zaben Majalisa, bayanai sun fito

NNPP ta lallasa jam'iyyu a Kano

A wani labarin, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana Alhassan Ishaq na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi ranar Asabar a mazabar Kura/Garun Mallam ta majalisar dokokin jihar Kano.

Baturen zaben Farfesa Shehu Galadanchi ya bayyana cewa Ishaq na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 37,262 inda ya doke Musa Daurawar na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 30,803.

Tun da farko dai kotun daukaka kara ta umurci INEC da ta sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 20 da ke mazabar Kura/Garun Malam a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel