Kano: A Karshe, Kotu Ta Dauki Mataki Kan Danbilki Kwamanda da Zargin Neman Ta da Husuma

Kano: A Karshe, Kotu Ta Dauki Mataki Kan Danbilki Kwamanda da Zargin Neman Ta da Husuma

  • Kotun Majistare da ke jihar Kano ta dauki mataki kan fitaccen dan siyasa, Abdulmajid Danbilki kwamanda
  • Kotun ta ba da belin dan siyasar kan naira miliyan daya da kuma gabatar da mai tsaya masa yayin da ba da belin
  • Wannan na zuwa ne bayan kama shi a ranar 23 ga watan Janairu kan zargin neman ta da husuma a jihar kan kalamansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, yana da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Kotun Majistare da ke Kano ta ba da beli ga fitaccen dan siyasa, Abdulmajid Danbilki Kwamanda kan kudi miliyan daya.

Jigon APC, Kwamanda an cafke shi ne a ranar 23 ga watan Janairu kan zargin neman ta da fitina inda aka tsare shi a gidan gyaran kaso.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya rufe wurin ibada kan damun jama'a da kara, ya gargadi mutane kan saba dokar

Kotu ta dauki mataki kan Dan Bilki Kwamanda a Kano
Kotu ta ba da belin Danbilki Kwamanda. Hoto: Getty Images, Wannan hoto an yi amfani da shi ne don misali kawai, ba shi da alaka da rahoton.
Asali: Getty Images

Wane mataki kotun ta dauka kan Kwamanda?

Yayin hukuncin, Mai Sahari’a, Abdulazeez Mahmud Habib ya ce tun da matsalar ta na da bukatar beli, an bai wa Kwamanda beli kan naira miliyan daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kotun ta bukaci Kwamanda ya kawo mai tsaya masa ko sakataren din-din-din da ke aiki a gwamnatin Kano ko wani basarake.

Sannan dole wanda ake zargin da kuma mai tsaya masa su ajiye fasfo din su ga kotun yayin ba da beli, cewar Daily Trust.

Har ila yau, kotun ta dage ci gaba da sauraran shari’ar har sai ranar 26 ga watan Faburairun wannan shekara.

Zargin da ake yi kan Kwamanda a Kano

Tun farko, mai gabatar da kara, Barista Bashir Sale ya ce ma'aikatar Shari'a a jihar ta nemi dauke shari'ar daga wurin 'yan sanda.

Har ila yau, wanda ake zargin ya ki amincewa da tuhume-tuhumen da ake yi kansa.

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta bada umarnin kama shugaban ma'aikatan gwamnan PDP da wasu mutum 5 kan abu 1 tak

Ana zargin kwamandan da wasu kalamai da suka saba wa doka a hira da gidan rediyo, cewar Vanguard.

Kwamanda ya kuma zargi tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso kan masarautun jihar wanda sanatan ya ce za a sake zama a kansu.

Danbilki zai ci gaba da zama a gidan kaso

Kun ji cewa jigon APC, Danbilki Kwamanda zai ci gaba da zama a gidan gyaran hali saboda cikas da aka samu.

Mai Shari'a, Abdulzeez Habib bai samu halartar zaman kotun ba wanda ya tilasta ci gaba da tsare Kwamanda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel