Korarren Kakakin Majalisa da Mataimakinsa Sun Dawo Kan Kujerunsu a Jihar Arewa, Bayanai Sun Fito

Korarren Kakakin Majalisa da Mataimakinsa Sun Dawo Kan Kujerunsu a Jihar Arewa, Bayanai Sun Fito

  • Korarren kakakin Majalisar jihar Bauchi ya samu damar dawowa kan kujerarsa bayan sake zabe a mazabar Ningi
  • Abubakar Suleiman na jam’iyyar PDP a samu nasarar ce bayan samun kuri’u 11,785 a zaben da aka gudanar
  • Ha rila yau, hukumar INEC ta ce dan takarar APC, Khalid Captain Ningi ya samu kuri’u 10,339 inda ya kasance na biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi – Tsohon kakakin Majalisar jihar Bauchi, Abubakar Suleiman ya sake dawowa kan kujerarsa bayan nasara a zabe.

Suleiman ya samu nasarar ce a zaben da aka gudanar a jiya Asabar 3 ga watan Faburairu a mazabar Ningi a jihar.

Korarren kakakin Majalisar jiha ya samu dawowa kan kujerarsa
Korarren Kakakin Majalisar Bauchi, Suleiman ya dawo kan kujerarsa. Hoto: Abubakar Suleiman.
Asali: Facebook

Mene Hukumar INEC ta ce kan zaben?

Kara karanta wannan

Aikin gama ya gama: Dan takarar PDP ya sha kaye a zaben cike gurbi a Yobe, an fadi wanda ya lashe

Yayin da ya ke sanar da sakamakon, Farfesa Ahmed Abdulhamid ya ce Suleiman na jam’iyyar PDP shi ne ya yi nasara a zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ahmed ya ce dan takarar ta PDP ya samu kuri’u 11,785 yayin da dan takarar APC, Khalid Captain ya samu kuri’u 10,339.

Idan ba a mantaba, Kotun Daukaka Kara ta rusa zaben kakakin Majalisar inda ta bukaci sake zabe a wasu rumfuna, TheCable ta tattaro.

Kotun ta umarci sake zaben ne a mazabu 10 a mazabar Ningi bayan dan takarar APC ya kalubalanci zaben.

Sauran sakamakon zaben da aka sanar

Har ila yau, Tsohon mataimakin kakakin Majalisar jihar, Jamilu Dahiru shi ma ya samu nasara a zaben mazabar Bauchi ta Tsakiya.

Yayin sanar da sakamakon zaben, Baturen zaben, Farfesa Isma’il Shehu ya tabbatar da Jamilu na jam’iyyar PDP wanda ya yi nasara.

Kara karanta wannan

INEC ta sanar da ɗan tsohon sifetan 'yan sanda wanda ya lashe zaben Majalisa, bayanai sun fito

Ya ce:

“Jamily Umaru Shehu ya samu kuri’u 45,240 yayin da ya doke abokin hamayyarsa, Aliyu Abdullahi Illelah na APC wanda ya samu kuri’u 40,266.

The Nation ta tattaro cewa jam’iyar PDP a jihar ta lashe dukkan zabukan da aka gudanar a kujeru hudu a jihar.

Wuraren da aka gudanar da zaben a Majalisar jihar sun hada da Bauchi da Zungur/Galambi da Ningi da kuma Madara/Chinade.

NNPP ta ci zabe a Kano

Kun ji cewa hukumar zabe ta INEC ta sanar da sakamakon zaben cike gurbi a jihar Kano.

Hukumar ta ayyana Bello Butu-Butu na jam’iyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Rimin Gado/Tofa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel