Karin Farashin Fulawa: Masu Yin Gurasa a Kano Sun Gudanar da Zanga-Zanga

Karin Farashin Fulawa: Masu Yin Gurasa a Kano Sun Gudanar da Zanga-Zanga

  • Dandazon mata da ke sana'ar sarrafa gurasa a Kano sun gudanar da zanga-zanga kan karin farashin kudin fulawa
  • Masu zanga-zagar sun koka kan yadda kudin buhun fulawa ya koma naira dubu 43 daga naira dubu 16 da suke siyansa
  • Wani dan kasuwa da Legit Hausa ta zanta da shi, ya ce ba laifin 'yan kasuwa ba ne kara farashin fulawar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - Wasu mata da ke yin gurasa a Kano, sun gudanar da zanga-zanga don nuna rashin jin dadinsu kan karin kudin fulawa.

Matan da suka gudanar da zanga-zagar a ranar Juma'a, sun ce karin kudin fulawar ya jefa sana'arsu cikin mawuyacin hali, rahoton Tribune Online.

Kara karanta wannan

Jerin kasashen duniya 5 da ya kamata ka ziyarta kafin su kara yawan jama'a

Masu yin ‘Gurasa’ a Kano sun gudanar da zanga-zanga.
Masu yin ‘Gurasa’ a Kano sun gudanar da zanga-zanga. Hoto: Tribuneonline
Asali: UGC

Gurasa dai na daga cikin nau'ikan buredi da ta yi shuhura a Arewacin Najeriya musamman Kano, inda ta zama abincin da aka fi sarrafawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matan da suka yi zanga-zangar, sun bi ta titin Yankusuma dauke da kwalaye masu rubutu daban daban a harshen Hausa.

Buhun fulawa ya haura naira 16

Wasu daga cikin abubuwan da aka rubuta a jikin kwalayen sun hada da:

"Ba mu yarda da karin kudin fulawa ba; tsadar fulawa na neman tsayar da sana'armu, BUA ka kawo mana dauki"

A cewar masu zanga-zagar, rayuwa ta yi tsada a Najeriya, inda suke gaza iya ciyar da iyalansu ko tura 'yayansu makaranta.

Da take magana da 'yan jarida, Hajiya Fatimah Anwar ta ce yanzu buhun fulawa ya kai naira dubu 43 maimakon naira dubu 16 da ake siyar da shi.

Kara karanta wannan

'Yan makarantar Ekiti: An bar yaranmu da yunwa sannan ga duka, Iyaye

Yan kasuwa ba su da laifi a karin kudin fulawa

Wani mai siyar da fulawa a jihar Kano, Alhaji Babangida mai fulawa, ya ce mutane da dama na dora alhakin hauhawar farashin kaya akan 'yan kasuwa, alhalin ba haka ba ne.

A zantawarsa da da Legit Hausa, Babangida mai fulawa ya ce su kansu 'yan kasuwa, na fuskantar kalubale idan farashin kayan ya karu, domin hakan na taba jarin su.

Ya ce:

"Matsalar tana wajen gwamnati da manyan kamfanoni, abin nufi, gwamnati ke da alhakin daidaita farashin dala akan naira, wanda kamfanoni ke amfani da farashin.
"A kwanan nan ka ga yadda dala ta haura har zuwa naira 1,600 a kasuwar bayan fage, wannan ya tilasta duk wasu kayan masarufi tashin gwauron zabi."

Haka zalika, Babangida ya ce mafi akasarin kamfanoni na amfani da injina na iskar gas, wanda farashinsa shima ya tashi, haka wajen safarar kayan hada fulawar.

Kara karanta wannan

Jerin kasashen duniya 6 inda rana ba ta faduwa, ga cikakken bayani

Ya yi kira ga gwamnati da ta samar da mafita kan hauhawar farashin dala wanda ke lalata harkar kasuwanci a kasar.

Kano: Mai gadin makaranta ya dauki rayuwarsa da kansa

A wani labarin, wani mai gadin wata makarantar kwaleji a Kano ya dauki rayuwarsa da kansa ta hanyar rataya.

An ruwaito cewa ya aikata hakan ne bayan samun labarin cewa tsohuwar matarsa ta sake yin wani sabon aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel