Sanatan Kano Ya Raba Gari da Shugaba Tinubu Kan Tsige 'Dan Arewa Daga Muhimmin Mukami

Sanatan Kano Ya Raba Gari da Shugaba Tinubu Kan Tsige 'Dan Arewa Daga Muhimmin Mukami

  • Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Kawu Sumaila, ya nuna adawa da yunkurin Shugaban kasa Bola Tinubu na sauke shugaban hukumar kula fannin albarkatun gas
  • Kawu ya ce rashin adalci ne matakin da Tinubu ya dauka na tube Kuliya daga mukaminsa wanda ya kamata ya yi shekaru biyar a kansa
  • Tinubu dai ya nemi a maye gurbin Kuliya wanda ya fito daga mazabar Kawu da Oluwole Adamu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Kawu Suleiman Sumaila, ya yi adawa da cire shugaban hukumar kula da fannin albarkatun gas, Mansur Kuliya, kafin cikar wa'adin shugabancinsa na shekaru biyar.

Kawu ya bayyana tsige Kuliya wanda aka nada a matsayin daraktan hukumar a 2022 a matsayin wanda baya bisa ka'ida.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya roki Tinubu ya dakatar da karin girma ga alkaliyar da ta rusa zabensa, ya fadi dalili

Kawu Samaila ya yi adawa da sauke Mansur Kuliya daga kujerarsa
Sanatan Kano Ya Raba Gari da Shugaba Tinubu Kan Tsige 'Dan Arewa Daga Muhimmin Mukami Hoto: @Dolusegun16/@MohmmedMasud
Asali: Twitter

Hakan ya biyo bayan bukatar da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike gaban majalisar, inda ya nemi a tabbatar da Oluwole Adamu a matsayin babban daraktan hukumar, rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ne ya karanto wasikar da ke dauke da bukatar Tinubu a zauren majalisar.

Wasu hujjoji Kawu Sumaila ya kafa?

Hakazalika, nan take Akpabio ya bukaci kwamitocin Gas da Fetur da su tantance sabon daraktan da aka zana sannan su mika rahotonsu ga majalisar a cikin mako guda, rahoton Daily Post.

Kawu ya ce:

"An nada wani daga mazabata a matsayin babban darakta kuma nadin nasa na shekaru biyar ne kamar yadda sashi na 34 (2), 5 da sashi na 36 (1) na dokar masana'antar fetur suka tanadar.
"Kuma hakan ya fara a watan Maris 2022 sannan majalisar dattawa ce ta tabbatar da shi kuma akwai tanadin doka da dama cewa idan har za a tsige shi ko maye gurbinsa saboda wani dalili, sai an bi tsari da ya yi daidai da doka da kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki yayin da almajiri da mai gadin makaranta suka dauki ransu a Kano

"Saboda haka, ina jan hankalin majalisar dattawa cewa nadin ko bawan Allah da ke kan wa'adin shugabancinsa, bai samu wata wasika na sallamarsa ko daga wani ba kawai ji ya yi cewa an sauke shi.
"Mu muka kafa wannan doka, hakki ne da ya rataya a wuyanmu mu mutunta ta."

Da yake martani ga Kawu, Akpabio ya bikaci kwamitocin da su duba ikirarin sanatan na Kano sannan su ba majalisar shawarwari kan mataki da gaba da ya kamata su dauka.

Me yan arewa suka ce?

Legit Hausa ta ji ta bakin wasu ‘yan Arewa kan wannan al’amari.

Abubakar Huzaifa ya ce:

“Gaskiya ya kamata a takewa Shugaban kasa Bola Tinubu burki kan wannan hanya da ya dauko.
“Mu ‘yan arewa mune muka yi ruwa muka yi tsarki wajen zaben Tinubu a 2023 amma sai dauki dai-dai yake yi mana a mukamanmu. Sai dauke ‘yan arewa ake yi ana maye su da ‘yan kudu.”

Kara karanta wannan

Daga dawowa zaman Majalisa, Tinubu ya bukaci ta amince da korar daraktan wata hukuma, ya nada wani

Muhammad Auwal kuwa cewa ya yi:

“Wannan ba sabon abu bane kowa nasa ya sani, amma dai a dunga yi ana sara ana duba bakin gatari. Ya kamata a kyale wadanda ke kan kujerar su gama wa’adinsu idan har ya zama dole sai an sauke su.
“Hakazalika ya kamata a dunga duba cancanta sama da komai wajen baya da mukami maimakon duba kabilanci ko wani abu.”

Tinubu ya sabonta nadin shugaban Hukumar NITT

A wani labarin, mun ji a baya cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Dr Bayero Farah a matsayin shugaban Hukumar Koyar Da Fasahar Sufuri a Najeriya (NITT), ta Zaria.

Mai magana da yawun hukumar, Mista John Kolawale, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Zaria, a ranar Juma'a, 19 ga watan Janairu, rahoton The Nation.

Asali: Legit.ng

Online view pixel