Abun Bakin Ciki
Matar marigayi tsohon shugaban Najeriya, Shehu Usman Aliyu Shagari ta rasu bayan fama da cutar korona. Hajiya Hadiza Shehu Shagari ta rasu ne a ɗaren Alhamis.
Wasu da ake zargin ‘yan asalin yankin Biyafara (IPOB) ne sun kashe jami’an ‘yan sanda hudu yayin da wasu suka kai hari kan ofishin ‘yan sanda da ke Anambra.
Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya jajantawa iyalan marigayi Malami Buwai, wanda ya rasu sakamakon doguwar jinya a ranar Litinin, 2 ga watan Agusta a Gusau.
Al’umomin da ke cikin Babban Birnin Tarayya (FCT) Abuja sun fara jin tashin hankalin barkewar cutar kwalara tare da rasa rayukan mutane akalla 60 ya zuwa yanzu.
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun harbe wani limamin cocin CRCN, Timothy Damisa, har lahira a Baissa, karamar hukumar Kurmi da ke jihar Taraba.
Labari da ke zuwa mana ya nuna cewa akalla dakarun sojoji 10 ne suka raya ransu a yau Alhamis, 24 ga watan Yuni bayan jirgin sojojin Kenya ya fado a yayin horo.
An kama wata mata da ake zargi da aikawa da mijinta barzahu bayan ta rafka mai tabarya a kai a karamar hukumar Kazaure da ke jihar Jigawa bayan sabani ya gibta.
Yan sa'o'i bayan mutuwar babban fasto, TB Joshuwa, wani faston Reverend Stephen Akinola, babban jagoran cocin Redemption Ministries Worldwide ya sake mutuwa.
Mohammed Babangida, dan tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Babangida, ya tsallake rijiya da baya lokacin da ayarinsa suka yi karo da tirela, an mutu.
Abun Bakin Ciki
Samu kari